Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA kotu ta daure tsohon Gwamnan Filato Joshua Dariye shekara 14 a gidan yari
bayan ta same shi da laifin cin amana da almubazzaranci.
Mai shari\’a Adebukola Banjoko ta samu Mista Dariye, wanda Sanata ne da ke wakiltar Filato ta tsakiya, da laifi a kan tuhumce-tuhumce 17 daga cikin 23 da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta zarge shi da aikatawa.
Laifukan sun hada da almubazzaranci da halatta kudin haram a lokacin da ya mulki jihar ta Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2007.
Sanata Dariye ya kasance cikin damuwa da dimuwa a lokacin da ake karanta hukuncin, ya nemi lauyan EFCC ya nuna tausayi da afuwa a matsayinsa na mai bin addinin Kirista.
Wannan hukunci na zuwa kwanaki kadan bayan da mai Shari\’a Banjoko ta daure tsohon Gwamnan Taraba Jolly Nyame shekara 14 a gidan yari saboda almubazzaranci da zamba da halatta kudin haram.
An yanke masa shekara 14 saboda cin amanar dukiyar jama\’a, sannan shekara biyu saboda almubazzaranci da dukiyar gwamnati.
Za a hade hukuncin wuri guda, wanda hakan ke nufin zai yi zaman jarum na shekara 14, kuma ba a bashi zabin biyan tara ba.
Mista Dariye ya yi shiru yana saurare a lokacin da ake karanta hukuncin a babbar