Isah Ahmed, Jos
Sir Joseph Ari shi ne Darakta Janar na asusun horar da ma’aikata na kasa [ITF] da ke garin Jos babban birnin jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa ya kamata kowane dan Nijeriya ya koyi sana’a, domin al’ummar Nijeriya sun fi na kowace kasa a duniya, bukatar koyon sana’o’i.
Har’ila ya bayyana cewa a cikin shekaru 2 asusun horar da ma’aikata [ITF] ya horar da ‘yan Nijeriya sama da dubu 150 sana’o’i daban daban.
Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
GTK; A wannan lokaci ne aka kafa wannan asusun horar da ma’aikata [ITF] kuma maye manufar kafa shi?
Joseph Ari; Shi dai wannan asusun horar da ma’aikata [ITF], wanda ke Karqashin ma’aikatar ciniki da masana’antu ta tarayya, an kafa shi ne a shekarar 1971 da manufar horar da al’ummar Nijeriya sana’o’i musamman daliban manyan makarantu da matasa maza da mata. Kuma hedkwatar wannan asusu tana garin Jos ne.
GTK; Wadanne irin nasarori ne kake ganin an samu musamman tun daga lokacin aka baka shugabancin wannan asusun horar da ma’aikata [ITF] shekaru 2 da suka gabata zuwa yanzu?
Joseph Ari; Babu shakka daga lokacin da aka nana ni shugaban wannan asusun horar da ma’aikata [ITF] zuwa yanzu wato shekaru 2 da suka gabata, mun sami nasarori da dama. Domin a lokacin da na karbi shugabancin wannan wuri na sami wurin a durkushe, amma sakamakon namijin kokarin da muka yi, mun sami nasarar sake tsarin tafiyar da wannan wuri, wajen cigaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda ya kamata.
Da zuwana wannan wuri a matsayin shugaba, abu na farko da na fara yi, shi ne gyara tsare tsaren yadda zamu yi aiki da kowanne dan Nijeriya a wannan wuri, domin wannan hukuma ce ta ‘yan Nijeriya gabaki daya. Wannan mataki da muka dauka, ya sanya mun sami nasarar hada kan dukkan ma’aikatan wannan hukuma.
Bayan haka a shekaru 2 da muka yi muna shugabancin wannan asusu, nasarar farko da muka fara samu, ita ce mun horar da ‘yan Nijeriya sana’o’i daban daban sama da duba 60, wadanda suka fito daga kungiyoyi sama da dubu 2. Har’ila yau mun sake horar da wasu matasa maza da mata sama da dubu 50 sana’o’i daban daban.
Haka kuma mun sake horar da wasu matasan sama da dubu 30 da suka fito daga jihohi 36 na tarayyar Nijeriya da babban birnin tarayya Abuja, sana’o’i daban daban da suka hada da dinki da walda da dai saurasu. Kuma dukkan wadannan matasa da muka horar, muna basu kyautar kayayyakin sana’o’in da muka koya masu, domin suje su bude wuraren sana’o’insu don su dogaro da kansu.
Har’ila yau mun horar da matan da suke zaune a yankunan karkara, sama da 500 sana’o’i kiwon kaji, gyaran gashi da kwalliya da dinki da gyaran wuta dai sauransu, a cibiyoyin horar da sana’o’i 32 da muke da su a kasar nan.
Haka kuma mun kirkiro wani shiri na koyar da sana’ar gini wanda muka fara a shekara ta 2017 a cibiyar horar da sana’o’inmu da ke Enugu.
A wannan shiri mun horar da ‘yan Nijeriya 1900 da suka fito daga jihohin Nijeriya 19 yadda ake aikin sana’ar gini da sana’ar kafinta da sana’ar gyara kayayyakin wutar lantarki.
A takaice daga lokacin da muka qarvi shugabancin wannan wuri zuwa yanzu shekaru 2 da suka gabata, wannan asusun horar da ma’aikata ya horar da matasan Nijeriya maza da mata sama da dubu 150 sana’o’i daban daban, ta hanyar tsare tsarensa na koyawa ‘yan Nijeriya sana’o’i.
A shekarar 1973 wato bayan shekaru 2 da kafa wannan asusu, an fito da shirin na horar da daliban manyan makarantu sana’o’i a wancan lokacin, wannan asusun horar da ma’aikata ya fara da daliban jami’o’i 11 da ke Nijeriya, kadai.
Amma yanzu maganar nan da muke yi da kai, akwai manyan makarantu 362 da suka hada da jami’o’i da makarantun kere kere da kwalejojin ilmi da miliyoyin dalibansu suka sami shiga wannan shiri.
Kuma mun sami nasarar raba kudade Naira Biliyan 1 da Nara Mliyan 600 ga manyan makarantu guda 328 don rabawa dalibai da malamai masu kula da su, da suka sami shiga wannan shiri koyawa daliban manyan makarantu sana’o’i kudaden alawus-alawus dinsu.
Har’ila yau wannan asusu ya yi hadin gwiwa da wasu hukumomi da kungiyoyi na duniya wadanda suka shahara wajen koyar da sana’o’i don yin aiki da wadannan wurare wajen koyar da al’ummar Nijeriya sana’o’i.
Babban burinmu kan wannan aiki da muka sanya a gaba shi ne mu juyar da hankalin mutanenmu daga sha’awar aikin gwamnati, wanda ba shi da tabbas. Su koma su mayar da hankalinsu wajen kama sana’o’in da za su dogara da kansu.
Yanzu wanda ya fi kowa kudi a Nijeriya bai taba aikin gwamnati ba. Wanda yafi kowa kudi a Afrika bai taba aikin gwamnati ba. Ya kamata ‘yan Nijeriya su fahimci cewa zasu iya rayuwa ba tare da aikin gwamnati ba.
Kuma mun dauki wannan mataki ne ganin cewa dukkan manyan kasashen da suka cigaba a duniya, sun sami cigaba ne sakamakon rungumar sana’o’i da al’ummominsu suka yi.
Idan ba a dauki wannan mataki na koyawa ‘yan Nijeriya sana’o’i ba, za a cigaba da samun matsalar rashin ayyukan yi a Nijeriya, domin hasashe ya nuna cewa nan da shekara ta 2025, al’ummar Nijeriya za su kai sama da miliyan 500. Kaga idan muka kai wannan matsayi za a sami miliyoyin ‘yan Nijeriya marasa ayyukan yi.
Amma idan muka koyawa ‘yan Nijeriya mutum miliyan 500 sana’o’i daban daban Nijeriya zata sami gagarumin cigaba a duniya.
Wannan shi ne babban abin da muka sanya a gaba a wannan asusun horar da ma’aikata.
Don haka, ina son nayi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar Nijeriya cewa mu yi gaggawar koya wa al’ummar Nijeriya sana’o’i. Domin Nijeriya tana bukatar al’ummarta su tashi su koyi sana’o’i fiye da kowace kasa a duniya. Domin dukkan karatun da ‘yan Nijeriya suke yi a makarantu, suna dogara ne da takardar kawai.
A Nijeriya akwai mutane da dama da suka yi karatun sana’o’i a makarantu amma ba su iya sana’o’in ba.
Bayan haka mun yi abubuwa da dama na kyautata rayuwar ma’aikatanmu a wannan hukuma.
GTK; Amma a baya mun sami labarin cewa wannan hukuma, tana da matsalar biyan kudaden ‘yan fansho wanne hali ake ci yanzu?
Joseph Ari; Babu shakka ada akwai matsalar biyan ‘yan fansho a wannan hukuma, amma da zuwanmu mun yi iyakar kokarinmu wajen warware wannan matsala. Domin daga lokacin da na karbi shugabancin wannan waje zuwa, mun yi kokarin karawa ‘yan fansho kudade sama da kashi 40 na kudaden da suke karba a da.
Bayan haka ya zuwa yanzu mun biya ‘yan fansho dukkan basussukan kudaden da suke bin wannan hukuma bashi. Don haka yanzu bamu da wata matsala ‘yan fansho a wannan hukuma.
GTK; Wadanne hanyoyi kuke bi wajen daukar wadanda kuke koyawa sana’o’i a wannan asusu?
Joseph Ari; Hanyoyin da muke bi wajen daukar wadanda da muke horarwa muna amfani ne da gwamnatocin jihohi ta hanyar tura takardun fom dinmu zuwa gwamnatocin jihohin, don kawo mana wadanda muke dauka. Kuma muna gaya masu su kawo mana wadanda suka cancanta.
GTK; Akwai ‘yan gudun hijira a sansanonin ‘yan gudun hijira musamman a yankunan arewa ta gabas sakamakon rikice rikicen da aka samu a wannan yanki, ko akwai wani shiri da wannan asusu yake yi wajen koyawa ‘yan gudun hijirar sana’o’i?
Joseph Ari; Dangane da koyawa ‘yan gudun hijira sana’o’i a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Kasar nan, tuni mun riga mun hada gwiwa da wasu kungiyoyi da hukumomi don ganin mun gudanar da wannan aiki. Sakamakon wannan hadin gwiwa da muka yi, a yanzu muna nan muna gudanar da aikin koyawa ‘yan gudun hijira sana’o’i a yankunan arewa ta gabas.
GTK; Karsher wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Nijeriya?
Joseph Ari; To kira na dai ga al’ummar Nijeriya kamar yadda nayi a baya, shi ne su rungumar sana’o’i. Ya kamata kowanne dan Nijeriya ko digiri nawa yake da shi, ya yi kokari ya rungumi sana’a.
Duk kasar da al’ummarta basu rungumi sana’o’i ba, za a sami matsala a tattalin arzikin wannan kasa.