MENE NE YA SAMU ZUMUNCINMU A YAU?

    0
    1885
    Kwamared Usman Nasidi
    Daga Kwamared Usman Nasidi
    ZUMUNCI ya kasance wani babban al\’amarin kuma mai matukar fa\’ida wanda Ubangiji Yake son al\’umma su kasance masu sada shi akodayaushe don karawa junansu dankon kaunar dake a tsakanin su da kuma kyautatawa junansu.
    A wasu yan shekarun baya, mutanen dori nada kokarin sada zumuncin ta inda har suke ziyartar junansu gari-gari don nuna irin mahimmancin da zumuncin ke dashi a tsakanin su kuma da nuna kaunarsu ga yan uwansu ko aminen arziki ba tare da yin la\’akari da nisan wajen ba ko wahalar da zasuyi na ganin sun sada wannan zumuncin ba, ballantana suyi tunanin abinda zasu kashe don zuwa wajen.
    Ga wasu kuwa, Zumunci ga wasu ya kasance wani babban al\’amari ne ayayin da suka dauke shi wani lalurar wajibi a garesu musamman a lokuta irin na bikin Sallah, inda yan uwa kan hadu a wurare daban daban ko su ziyarci juna a gidajensu domin sada wannan zumuncin tare duk iyalen su a yayin zuwa sada shi, domin wasu ma kan kai ziyara har zuwa wasu garuruwa masu nisa don ganin yan uwa su na nesa banda na cikin garin da suke.
    Zumunci ya kasance yayi tasiri mai karfi har izuwa karni na ashirin dukda kasancewa zamani na ta chanzawa kuma ana ta samun cigaba ta fannin rayuwa ta yadda mutane kan iya sada zumunci ba tare sun kai ziyara har zuwa wasu garuruwa masu nisa ba, toh amma dukda hakan wasu basu yarda al\’adarsu ta zuwa kai ziyara wasu wuraren masu nisa ba.
    Wato wani babban abin sha\’awa da sada zumunci shi ne yan uwa zasu ga juna ido da ido kuma zasu zanta domin babu wanda yasan lokacin da zasu sake haduwa baya ga ladan da zasu samu na sada wannan zumuncin, dukda babu wanda yasan ko da rabon su sake haduwa idan rai ya yi halin shi a tsakanin su domin wasu a hanyarsu ta sada zumuncin ko wajen tafiya ko dawowa rai ke yin halin shi.
    Toh amma a wannan karnin da muke a yanzu, zumunci ya kasance wani babban al\’amarin takaici a cikin al\’umma saboda basa la\’akari da irin fa\’idar shi wanda hakan yake sanya shi gagarar wasu domin su sada shi a sakamakon wasu yan matsaloli ko lalurorin da suke a tattare da al\’umma duk ta yadda sukayi ra\’ayin sada shi amma suke hakura dashi saboda babu yadda za suyi, to amma ga wasu kuma ba haka bane domin basu da wannan al\’adar ko ra\’ayin sadar da shi domin basu dauke shi da mahimmanci ba.
    Hakan kuwa ya sanya a wannan zamanin da muke, zumunci ya tabarbare ta yadda za kaga dukda irin na\’urorin sada zumuncin na zamani, jama\’a da dama basa kokarin sada shi tamkar yadda mutanen dori ke yi, don za kaga wasu basa iya ko dan kokarin kiran wasu a wayar tafi da gidanka wato Salula, balle har suyi kokarin zuwa kai ziyara a gidajesu ko su tura iyalen su gidajen yan uwansu na kusa bayan su ba irin wannan tarbiyar aka basu ba.
    Wani babban abin al\’ajabi a wannan zamanin da muke shi ne zumuncin ma an raba shi izuwa kashi-kashi ta inda za kaga \’ya\’yan masu hannu da shuni basa ziyartar yan uwansu wadanda ba masu hali ba sai idan an hadu a wata lalurar ta dole ko kuma akan hanya sannan ayi zumuncin, ko kuwa kaga idan an hadu a wajen wata lalurar kaga wasu sun ware gefe daya saboda basa son saka kansu cikin \’yan uwansu da basu da hali ko kaga suna gudun su ko kyamatarsu.
    Wannan lamarin ya sanya wasu \’ya\’yan zamanin yanzu basa sanin junansu balle har su kaunaci junansu ta yadda zasu rika sada zumunci a tsakanin su wanda hakan ke mayar dasu baki a tsakanin junansu akodayaushe, musamman ganin yadda iyayensu ke hulda da sauran iyayen sauran yaran ko kuwa suke nunawa a idon jama\’a idan sun hadu a wajen wata lalurar.
    Alalhakika, zumunci a halin yanzu ya dauko hanyar tabarbarewa ta yadda ko ziyarar da yara keyi izuwa gidajen yan uwansu a lokutan bikin Sallah ko da ko sunyi aure ya canza sabon salo, domin mafi akasarin yara basa ziyartar junansu da sauran danginsu, saidai gidajen iyayensu dana surukansu kawai wanda iyayensu ba bisa irin wannan turbar suka taso ba.
    Ya Ku juma\’a ku sani, ya kamata ku gyara tarbiyar zumuncin dake tsakaninku domin yaran yanzu sai anyi dagaske ake dorasu a bisa hanya saboda wasu yaran ma dukda irin kokarin da iyayensu ke yi na nuna musu fa\’idar zumuncin, basa kokarin bin wannan hanyar da ake nuna musu koda ko sunga iyayen na kokarin sada zumuncin ballantana ace iyayensu ba masu son sada zumuncin bane wanda hakan zai basu damar kauracewa duk wasu yan uwansu da suka sani balle wadanda basu sani ba.
    A karshe ya ku iyaye, inaso na kara tunatar da Ku cewa Ubangiji baya son duk mai yanke zumunci kuma sada zumunci wata hanya ce ta samun wani babban ladan dakan iya kai mutum ga babban rabo a ranar gobe kiyama, don haka ku kyautata zumuncin dake tsakanin ku kuma ku lurar da \’ya\’yanku akan wannan hanya ta sada zumunci domin su kaunaci junansu da sauran yan uwansu da danginsu baki daya ba tare nuna wani wariya ba ko nuna banbancin launin fata ba.
    Ya Allah Yasa mu dace kuma Ya bamu ikon yin zumuncin ta yadda ya dace.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here