Isah Ahmed, Jos
SHUGABAN majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga gwamnati, kan ta yiwa alhazan Nijeriya rangwame kan kudin aikin hajji. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake rufe tafsirin Azumin watan Ramadan da ya gabatar a garin Jos.
Ya ce wannan kira na a yiwa alhazai rangwame don su sami damar gudanar da aikin hajji cikin sauki yana da matukar mahimmanci, domin aikin hajji yana daya daga cikin shika shikan addinin musulunci.
Har’ila yau ya yi kira kan a rika nada malaman addinin musulunci a matsayin jagororin alhazai a maimakon a rika nada wadanda basu da ilmin addinin musulunci, a matsayin jagororin alhazai.
Ya ce sam wannan bai dace ba domin jagorancin aikin hajji aiki ne na malaman addinin musulunci, ba aikin ne na wadanda basu da ilmin addinin musulunci ba. Ya kamata malaman addinin musulunci su fito su yi magana kan wannan al’amari domin aikin jagorancin alhazai aikin su ne.
Sheikh Jingir ya bukaci a rika yiwa dukkan wanda aka samu ya shigo da miyagun kwayoyi Nijeriya hukumci mai tsanani, domin ya zama darasi.
Ya ce masu shigo da miyagun kwayoyi suna cutar al’ummar Nijeriya, ta hanyar haukatar da mutanenmu. Saboda haka a duba shagunan masu sayar da magunguna na Nijeriya, don gano masu sayar da miyagun kwayoyi ga jama’armu.
Yace babu shakka a halin da ake ciki matsalar shaye shayen miyagun kwayoyi a Nijeriya, ana son a ci mutanen Nijeriya da yaki ta hanyar haukatar da jama’armu. Don haka ya kamata gwamnati ta dauki tsauraran matakai na magance wannan matsala.
Sheikh Jingir ya yabawa gwamnati kan nasarorin da take samu kan tsaro a kasar nan. Don haka ya yi kira ga gwamnatin kan ta kara inganta tsaro a Nijeriya.
‘’Tsaron nan na kowanne xan Nijeriya ne bana gwamnati ne kadai ba. Don haka ya kamata dukkan al’ummar Nijeriya su zamanto masu lura da abubuwan da suka shafi tsaro a kasar nan, don mu bada gudunmawarmu wajen magance matsalar tsaro a kasar nan.