Isah Ahmed, Jos
KARAMAR hukumar Lere da ke jihar Kaduna ta bayar da akin gyara wutar lantarkin yankin da ta yi wata da watanni a lalace. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Abubakar Buba ne ya bayyana haka lokacin da yake rantsar da kansilolin karamar hukumar a garin Saminaka.
Ya ce ganin irin mawuyacin halin da al’ummar wannan karamar hukuma suka shiga, sakamakon lalacewar wutar lantarkin wata da watanni ya sanya suka bayar da aikin gyaran wutar.
Har ila yau ya ce za su biya dukkan wadanda suke bin karamar hukumar bashi. Ya ce amma idan suka biya wadanda suke bin karamar hukuma basussukan kudaden da suke bi, dole ne duk mutumin da aka biya, ya tsaya ya yi aikin da aka ba shi. Duk wanda aka biya shi hakkinsa, yaki ya tsaya ya yi aikinsa, to karamar hukumar zata dauki mataki a kansa.
‘’ A wannan karon za a yi tsarin majalisun dokoki da majalisun zartarwa a kananan hukumomin jihar Kaduna. Don haka yanzu kansiloli za su rika yin zama, suna tsara dokoki a kananan hukumomin jihar. A yayin da shugabannin kananan hukumomin jihar da ‘yan majalisar zartarwarsu za su rika zama, suna zartar da al’amuran da suka shafi kananan hukumominsu’’.
Alhaji Abubakar Buba ya yi bayanin cewa za su tafi da kowa da kowa a karamar hukumar Lere. Kuma za su yi dukkan abin da jama’a suke so, don haka ya yi kira ga jama’ar karamar hukumar su ci gaba da basu goyan baya da hadin kai, domin su sami nasara kan kudurorin bunkasa karamar hukumar, da suka sanya a gaba.
A wajen taron shugaban karamar ya bayyana sunayen nadadun kansiloli da za su kula da ma’aikatun karamar hukumar da sakataren karamar hukuma.Nadadun kansilolin sun hada da mataimakinsa Magaji Musa Buba da Shehu Mato da Malam Nuhu Ustaz Kayarda da Idris Hamisu. Sakataren karamar hukumar kuma shi ne Sulaiman Tambaya.
Har ila yau a wajen taron majalisar kansilolin karamar hukumar 11, sun zabi shugabanninsu inda suka zabi Honarabul Sadiq Abubakar a matsayin shugaban majalisar, Honarabul Luka Wali mataimakin shugaba, Sulaiman Maiwada Lere shugaban masu rinjaye, Honarabul Salisu Musa mai tsawatar wa majalisar.