Daga Usman Nasidi
HUKUMAR ‘yan sanda reshen jihar Kaduna ta sanar da haramta duk wani nau’in taron jama’a gabanin gurfanar da shugaban kungiyar mabiya shi’a na Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky, a dukkan lokutan da za a shiga shari\’arsa .
A wani jawabi da hukumar ta fitar ta ofishin kakakinta, Mukhtar Aliyu, ta bayyana cewar za ta zuba jami’anta a kowanne lungu da sako na garin Kaduna muddin za a yi shari\’ar saboda kare rayuka da dukiyoyin al\’umma.
Ya ce magidanta su saka idanu sosai a kan unguwannin da suke tare da bukatarsu da sanar da hukuma duk wani motsin jama’a da basu amince da shi ba.
“Muna sanar da mutanen garin Kaduna masu biyayya ga doka da kada su tayar da hankalinsu domin zamu tabbatar da ba a samu barkewar wani tashin hankali ko rikici ba,” a cewar Aliyu.
Aliyu ya jaddada cewar yin kowanne irin nau’in taro bai halasta ba tare da sanar da cewar kuma hukumar ‘yan sanda zata gauraya ga duk wanda ya saba doka da oda.