ULAMA TA BUKACI A KAWO KARSHEN KASHE RAYUKAN DA AKE YI A NIJERIYA  

0
563
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir.

 Isah Ahmed, Jos

MAJALISAR kungiyoyin addinin musulunci da ke jihar Filato, da ake kira\’\’Plateau State Council of Ulama\’\’ ta bukaci a kawo karshen kashe kashen  rayukan da ake yi a Nijeriya. Majalisar ta bayyana wannan bukata ce,  a wata sanarwa da shugaban majalisar  Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya fitar a garin Jos, kan rikicin da ya faru a jihar Filato, a makon da ya gabata.

Sanarwar da mataimakin sakataren majalisar Honarabul Ahmad Ashiru ya sanyawa hannu, ta ci gaba da cewa hare haren ramuwar gayyar da ya yi sanadin asarar rayukan mutane da dama da dukiyoyi masu tarin yawa a rikicin da aka yi  a jihar Filato, a makon da ya gabata wani babban abin Allah wadai ne.

Majalisar  ta nuna takaicinta kan tashin wannan rikici na jihar Filato, musamman ganin irin zaman lafiyar da aka samu a jihar, bayan rikice rikicen da jihar ta yi fama da su a shekarun baya.

Majalisar ta bukaci gwamnati da sauran ‘yan siyasar Nijeriya su dauki matakan kawo karshen kashe kashen rayukan da ake yi a Nijeriya.

Majalisar ta ce abin bakin ciki ne a ce a kasa kamar Nijeriya, a hana  mutane bin wasu hanyoyi. Don haka ta bukaci gwamnati ta yi doka mai tsanani kan masu tsare hanya suna kashe mutane, a yayin da da suke tafiya.

Har ila ya majalisar ta bukaci gwamnati ta zuba ido a wuraren da ake samun tashin hankali a kasar nan, kamar jihohin  Filato da Zamfara da yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here