Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban \’Yan Sanda Rasuwa

0
722

 

Mustapha Imrana Abdullahi Da Usman Nasidi Daga Kaduna

TSOHON shugaban \’yan sandan Nijeriya kuma shugaban kungiyar tuntubar ta Dattawan Arewa, kana Sardauna Katsina Alhaji Ibrahim Kumasi, ya rasu.

Sanarwar ta fito ne daga bakin kanen marigayin Alhaji Dahiru Kumasi, kuma ya tabbarar wa manema labarai hakan.

Inda ya ce za a yi jana\’izarsa a masallacin Juma\’a na Babu Kumasi da ke unguwar Turawa ta Katsina.

Kafin rasuwarsa, marigayin ya yi aiki a karkashin mulkin soji na marigayi Sani Abacha da Janar Abdulsalamu a shekarar 1993 zuwa 1999.

Tsohon shugaban \’yan sandan Najeriya IG Ibrahim Kumasi dan kimanin shekaru 76 a duniya kafin rasuwasa, ya rasu ne a wani asibiti da ke jihar Katsina, inda ya bar mata daya da yara shida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here