KADA AL’UMMAR NIJERIYA SU AMINCE A KIRKIRO ‘YAN SANDAN JIHOHI-SHEIKH JINGIR

0
672
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir,,,,,

 Isah Ahmed, Jos

SHUGABAN majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya gargadi al’ummar Nijeriya kada su yarda a kirkiro ‘yan sandan jihohi a Nijeriya. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi a masallacin juma’a na ‘yan taya da ke garin Jos.

Ya ce ya  kamata al’ummar Nijeriya su fito su gayawa shugaban kasa da gwamnoni da ‘yan majalisun kasa kan ba su yarda a kirqiro ‘yan sandan jihohi ba. Domin ana son a yi barna da wadannan ‘yan sandan jihohi ne a cuci talakawan Nijeriya.

Ya ce babu shakka idan aka bai wa gwamnoni dama su yi ‘yan sandan jihohi, ba za a sami zaman lafiya ba a Nijeriya, domin wasu gwamnonin za su yi amfani da wadannan ‘yan sanda wajen cutar da al’ummomin jihohinsu.

‘’Don haka kungiyar Izala ba ta goyi bayan a yi ‘yan sandan jihohi ba. Muna sheda wa shugban kasa da  majalisun kasa  kan cewa bamu goyi bayan a yi ‘yan sandan jihohi ba. Domin akwai hadari tattare da wannan shiri’’.

Sheikh Jingir ya yaba wa shugaban kasa Muhammad Buhari kan kokarin da yake yi wajen dawo da kudaden kasar nan da aka sace aka kai kasashen waje. Ya ce ba a taba samun shugaban da aka dawo da kudaden Nijeriya da aka sace kamar shugaban kasa Buhari ba.

Har ila yau ya yaba wa shugaba Buhari kan kokarin da ya yi wajen bunkasa harkokin noma da dawo da maganar aikin jawo ruwan teku zuwa arewa da maganar kaddamar  aikin jirgin kasa da sauran ayyukan raya kasa da ya sanya a gaba.

Daga nan ya yi kira ga ‘yan siyasar Nijeriya kan su   hada kai suyi siyasa don Allah domin a sami zaman lafiya da cigaba a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here