Isah Ahmed, Jos
SHUGABAN kungiyar tabbatar da adalci da tsaro da tattaunawa tsakanin al’ummomin da suke rikici [JSDC ]da ke garin Jos babban birnin jihar Filato, Alhaji Lawal Baba Otu ya bayyana cewa shaye shayen miyagun kwayoyi da matasan kasar nan, suke yi ne yake kawo ayyukan ta’addancin da ake fama da su a kasar nan. Alhaji Lawal Baba Otu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce matsalar shaye shayen miyagun kwayoyi, matsala ce da take damun al’ummar kasa gabaki daya. Kuma mafiyawaci matasa ne suke shaye shayen wadannan miyagun kwayoyi.
Ya ce idan aka cigaba da barin matasan kasar nan suna shaye shayen miyagun qwayoyi, ba zasu amfani kansu ba, kuma ba zasu amfani kasa gabaki daya ba.
Alhaji Baba Otu ya yi bayanin cewa miyagun kwayoyin nan a cikinmu ake sayar da su. Domin a kowace unguwa akwai masu sayar da irin wadannan miyagun kwayoyi, ta hanyar fakewa da shagunan sayar da magunguna.
Ya ce a wadannan shagunan sayar da magunguna da suke unguwanninmu, a wajensu ake samun irin wadannan miyagun kwayoyi.
Alhaji Baba Otu ya ce ganin irin illolin da shaye shayen miyagun kwayoyi, ya sanya kungiyarsu ta tashi tsaye wajen wayar kan jama’a kan illolin shaye shayen miyagun kwayoyi a garin Jos da kewaye.
‘’A wannan garin na Jos mun ziyarci makarantun sakandire na GSS West Of mine da GSS Unguwar rogo da GSS Gwom, mun wayar wa da dalibai kai, kan illolin shaye shayen miyagun kwayoyi. Haka kuma mun ziyarci unguwannin da dama da wuraren da matasa suke zama a wannan gari, mun wayar masu da kai kan illolin shan miyagun kwayoyi’’.
Alhaji Baba Otu ya yaba wa gwamnatin jihar Filato kan kokarin da ta yi wajen ganin an sami zaman lafiya a jihar. Ya ce babu shakka gwamnan jihar Filato ya yi kokari wajen samar da zaman lafiya a jihar Filato.
Ya ce amma a hana shigo da miyagun kwayoyi a jihar, shi ne zai kawo tabbatatcen zaman lafiya da bunkasar arziki a jihar.
Ya yi kira ga al’ummar Nijeriya kan kowa ya tashi ya bada gudunmarsa, wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.