An Fatattaki \’Yan Najeriya Daga Kasar Sin

0
848

 

Daga Usman Nasidi

WANI faifan bidiyo mai tayar da hankali da ke yawo yanzu haka a kafafen sadarwar zamani a Najeriya na nuni ne da yadda wasu \’yan Najeriya suka yi cirko-cirko a saman titi a gaban wani Otel din kasar Sin biyo bayan umurnin jami\’an \’yan sandan kasar.

Kamar yadda muka samu labarin, an ce \’yan sandan kasar ta Sin ne suka bayar da umurni ga dukkan masu otel din kasar su fitar da \’yan Najeriyan da ke cikinsu saboda wani boyayyen dalilin da har yanzu ba a bayyana ba.

Rahotanni na bayyana cewar wasu \’yan Najeriya din dai sun nuna matukar rashin jin dadin su game da wannan matakin da gwamnatin ta dauka kansu musamman ma ganin cewa su mutanen kirki ne da suka zo kasuwanci kawai.

A cikin faifan bidiyon haka zalika an ga wani jami\’in gwamnatin Najeriya da ke aiki a ofishin jakadancin kasar yana kwantar masu da hankali tare da shan alwashin bin kadin lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here