An Harbe Babban Limanin Garin Bachi

0
882
Daga Usman Nasidi

A daren ranar Laraba ne wasu \’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe babban limamin garin Bachi da ke karamar hukumar Riyom na jihar Filato.

Marigayi Alhaji Abdullahi Abubakar ba boyeye ba ne a jihar musamman yadda ya yi suna wajen kira a zauna lafiya da kuma hallartan taron sulhu tsakanin Fulani da \’yan kabilar Birom da masu sassan jihar.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Ibrahim Mato, ya shaida wa GTK cewa marigayi Abubakar mutum ne mai son zaman lafiya da hadin kan al\’umma hakan ya sa kowa ke mutunta shi.

Ya ce \’yan bindigan sun kutsa kai ne cikin gidan babban malamin misalin karfe 10 na dare kuma suka harbe shi har lahira.

Jami\’an yadda labarai na Operation Safe Haven, Manjo Adam Umar, ya ce shugaban kungiyar Miyetti Allah na Riyom ya kawo masa rahoton rasuwar.

Ya kara da cewa jami\’an hukumar sojin sun fara gudanar da bincike tare da \’yan sanda don ganin an gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.

A wani rahoton, NAIJ.com ta kawo muku rasuwar tsohon Sufeta Janar na \’yan sandan Najeriya, Alhaji Ibrahim Coomassie, marigayin ya rasu ne a jiharsa ta Katsina bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Anyi jana\’izar Coomassie a ranar Juma\’a 20 ga watan Yulin shekarar 2018 a jihar Katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here