‘’Za Mu Ba Da Ingantaccen Wakilci A Majalisar Dattijai – Dokta Salisu Ahmed Ingawa

0
815

Zubair A Sada, Daga Kaduna

‘’BABBAN abin da na gani a yankin dan Majalisar Dattijai na Katsina ta Arewa wanda har ya tsima ni nake son in fito takarar kujerar Sanata mai wakiltar mazabar shi ne, rashin aikin yi ga manya da matasanmu, in nema masu ayyukan noma ne, ‘yan sanda ne, soja , jami’an kwastan da na shige da fici (immigration) da sauran ayyukan yi da dama’’.

Wannan batu ya fito ne daga bakin Dokta Salisu Ahmed Ingawa a yayin da yake tattaunawa da wakilanmu a yau Asabar 21 ga watan Yuli 2018 a Kaduna.

Dokta Salisu Ingawa ya ci gaba da cewa, ya shiga wannan yanki nasu lungu-lungu a dukan mazabarta tasu tad an majalisar mai kananan hukumomi 12, inda ya nuna takaicinsa da damuwarsa kan yawa-yawan rashin aikin yi day a dabaibaye al’ummomin yankin. Manyan mutane babu kudaden da za su yi wadataccen noma, babu taki da sauransu, matasa kuma bas u da isassun ayyukan yi,

Dan takarar kujerar Sanatan na Katsina ta Arewa a tutar jam’iyyar APC wanda har ila yau kwararren masani ne a fannin noma, ya ce ko shakka babu idan Allah ya nufa ya kai shi Majalisar Dattijai zai bada shawarwari sosai don ganin yadda za a shawo matsalolin rashin ayyukan yi. Haka kuma zai bai wa manoma shawarwarin yadda za a sami taki da iri nagari da muhallin shukar kansa da ma yadda za a sarrafa kayan nomad a yadda za a adana su. Ya ce ita kuma gwamnati a bangarenta ya dace ta dinga sanya farashin kayayyakin albarkatun noma tun kafin a yi shuka, ta fadi farashin dukan nau’o’in dukkan abin da mutum ya noma, sannan za a saya.

Da yake tsokaci a kan ko hukumar adana kayan abinci ta kasa inda ya shugabanta kuwa, Dokta ingawa cewa ya yi, hukumar na nan ba ta mutu ba, duk rumbunan da aka yi suna nan daram, sai dai babu kayan abinci a cikinsu, rashin kudade ne kawai ya kawo ba ta yi aikinta sosai ba, saboda gwamnati na fuskantar matsalolin boko haram da ‘yan gudun hijira, inda take bukatar kudaden da za ta ciyar da su abinci, hakan ya hana gwamnatin yin amfani cikakke da hukumar.

Magoyin bayan shugaba Muhammadu Buhari da ya juya don amsa wata tambaya kan Gwamna Aminu Bello Masari kuwa, sai ya ce, Gwamna Masari yana kokari kuma ya yi kokari  domin kuwa ya jajirce kan samar da cikakken  tsaro inda ta kai har teburin sulhu ya zauna kuma daga wannan zama aka ajiye makamai a jihar Katsina, Sannan ya gayyato Songhai da Dangote domin zuba jarinsu, ga kuma taki ga manoma, ga titunana a karkaru da dama da sauransu. Ya ce ita ma gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari batun na boko haram ya zama tarihi sai abin dab a a rasa ba a can Maiduguri da sabon salon fadan Fulani da manoma wanda kusan akwai alamar siyasa cikinsa.

A wannan gabar ne dan takarar kujerar Sanatan Katsina ta Arewa, Dokta Ingawa ya nemi ‘yan majalisar kasa da fadar shugaban kasa da su bi a hankali su hada kawunanasu waje daya su duba tare da tunkarar duk wani abin da zai taso, muddin suna yin haka to, tabbas za a sami mafita.

Daga karshe ya gode wa al’ummar yankin mazabarsa da na jihar Katsina kwata da ma na kasa baki daya, inda ya ce tsarin da aka kawo na yin zabe kai tsaye abu ne mai kyau, duk kowa mai katin zabe ya zabi abin da yake so, idan ma Deligates ko Exco ne za su yi zaben su ma akwai lokacin da ake ganin nasu zaben yana da kyau. Sai ya yi addu’ar Allah ya yi mana zabin alheri baki daya a rayuwarmu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here