Gobara Ta Lashe Shaguna A Kasuwar Jos

0
629
NDLEA na kona miyagun kwayoyin da suka kama
Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA mummunar gobara ta lakume shaguna da runfuna da dama a babbar kasuwar Terminus a garin Jos.
Gobarar ta yi sanadiyar hasarar dukiya mai yawa kamar yadda daya daga cikin \’yan kasuwar da gobarar ta shafa ya shaida wa  manema labarai.
\”Gobarar ta tashi ne kusan misalin karfe biyu na dare a bangaren da ake kira Baluje a babbar kasuwar ta garin Jos.\” in ji shi.
Ya ce gobarar ta ci runfunan \’yan kasuwa na wuccin gadi da dama wadanda har yanzu ba su iya kayyade adadinsu ba, sannan kuma ta taba wasu shaguna a kasuwar.
Kuma ya ce har yanzu ba a gano musababin gobarar ba, saboda a cikin tsakiyar dare ne
gobarar da ta fara ci.
Kwamishinan \’yan sandan jihar Undie Adie ya shaida wa manema labarai cewa sun samu
labarin gobarar lokacin da ta fara tashi kuma nan take suka sanar da jami\’an kashe gobara
wadanda suka yi kokarin takaita al\’amarin.
Kawo yanzu babu rahotannin hasarar rayuka da aka samu sakamakon gobarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here