Rabo Haladu Daga Kaduna
JIGILAR maniyata zuwa aikin farali na Hajj ta kankama a inda daga jihar Kogi kimanin 446 suka tashi daga Abuja zuwa birnin Madina a ranar Asabar wanda nan ne shiyyar farko da aka fara tashi a hajjin bana,
Jirgin Max air ne ya fara jigilar maniyatan wadanda suka kunshi maza 228 da kuma mata
218, kamar yadda hukumar alhazzai ta kasa NAHCON ta wallafa a shafinta na Twitter.
Ministan Abuja Musa Bello ne ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kaddamar da fara aikin jigilar maniyatan zuwa Saudiyya.
Shugaban kasa ya jaddada tabbatar da tsaron alhazzan na Najeriya da kare lafiyarsu a
dukkanin kwanakin da za su kwashe suna ibadah a Saudiyya har zuwa dawowarsu.
Daga yanzu za a ci gaba da jigilar maniyatan a sassan jihohin Najeriya zuwa kasar Saudiyya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, jakadan Najeriya a masallatai ma su tsarki na Makkah da
Madina, Adnan Mahmoud Bastaji ya ce an fara jigilar maniyatan ne bayan hukumomin Saudiyya sun sanar da kammala shirye-shiryen karbar maniyata aikin hajji.
\”An samar da dukkanin abubuwan da suka dace domin karbar maniyata aikin hajji daga sassan duniya a biranen Madina da kuma Makkah.\” in ji shi.