Al\’ummar Dawakin Tofa Sun Gode Wa Sakataren Hukumar Makarantun Kimiyya Da Fasaha Na Jihar Kano.

0
704
Gwamna Ganduje Na Jihar Kano
Jabiru Hassan, Daga Kano
AL\’UMMAR karamar hukumar Dawakin Tofa sun jinjinawa babban sakatare na hukumar makarantun kimiyya da fasaha na jihar kano, Alhaji Ahmad Tijjani Abdullahi (ES) bisa kokarin da yake yi wajen tallafawa ilimi a yankin.
Sunyi wannan yabo ne a cikin wata takarda da suka baiwa wakilin mu, inda suka nunar da cewa babban sakataren yana kokari sosai wajen ganin ilimi a karamar hukumar Dawakin Tofa yana kara bunkasa musamman ganin yadda gwamnatin jihar kano take baiwa fannin ilimi kulawa ta musamman.
A cikin takardar, wadda Malam Sulaiman Adamu  ya sanya wa hannu a madadin iyaye da masu rike da yara na yankin, ta bayyana cewa ko shakka babu  al\’umar karamar hukumar  Dawakin Tofa  suna alfahari da gagarumar gudummawar da  Alhaji Ahmad Tijjani Abdullahi yake baiwa ilimi a yakin, tareda fatan cewa sauran masu rike da mukamai na gwamnati zaau yi koyi da shi kamar yadda ake gani a zahiri.
Daga karshe sun bayyana babban sakataren a matsayin wanda yake bin sahun gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje wajen ciyar da ilimi gaba kamar yadda ake bukata, tare da fatan cewa iyaye da malaman makarantu za su yi amfani da kayayyakin da aka ba su wajen bada tasu gudunmawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here