An Yi Jana\’izar Farfesar Da Barayi Suka Kashe A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

0
570
Rabo Haladu Daga Kaduna
RUNDUNAR \’yan sandan jihar Kaduna  ta ce akalla mutum hudu ne aka kashe a lokacin
da wasu barayi suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Cikin mutanen da aka kashe a harin na ranar Lahadi, har da Tsohuwar Kwamishinar Ilimi ta
jihar Katsina Farfesa Halimatu Idris, kamar yadda \’yarta ta tabbatarwa da manema labarai
Sai dai rundunar \’yan sandan ba ta bayyana sunaye ko yankunan da wadanda suka mutu suka fito ba.
Ba ya ga mutanen da aka kashe, bayanai sun kuma ce barayin sun yi garkuwa da wasu karin mutane, a harin wanda aka kai tsakanin garin Jere da Katari.
An dade ana garkuwa da jama\’a domin neman kudin fansa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, abin da yake ci gaba da ciwa matafiya tuwo-akwarya.
\’Yan kasa da dama na sukar yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke tunkarar
lamarin, amma jami\’ai sun sha nanata cewa suna iya kokarinsu.
Diyar marigayiya Farfesa Halimatu, ta shaida wa Manema labarai  cewa mahaifiyarta ta tashi ne daga Kaduna zuwa Abuja  a ranar Lahadi.
A wannan hali ne kuma kwararriyar malamar makarantar ta hadu da ajalinta.
\”Muna gida aka ce min na tafi Katari, sai na taras da ita a wani asibiti da harbin bindiga, tana tari da korafin cewa tana jin zafi\”.
Ta kara da cewa \”ta shafe dogon lokaci kafin a dauke ta zuwa asibiti saboda rashin motar
daukar marasa lafiya, kuma kafin mu kai asibitin Allah ya yi mata cikawa\”.
A ranar Litinin ne aka yi jana\’izar marigayiyar a birnin Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa\’i ya wallafa a shafin Twitter cewa \”yana aiki tare da gwamnatin tarayya domin kawo karshen sace-sace da fashi da makami a jihar. Ko wanne rai na da matukar muhimmanci:
Masu lura da al\’amura na ganin wannan ba karamin rashi ba ne musamman ga fannin ilimin yankin arewacin Najeriya, ganin cewa ba kasafai ake samun mata da suka kai matakin ilimi na Farfesa ba a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here