\’\’Ban Goyi Bayan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Ya canza Sheka Ba\’\’- Farfesa S A Yakasai

0
747
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na Jihar Sakkwato dan takarar shugaban kasa a jam\'iyyar PDP

Rahoton Zubair A Sada
TSILLA-TSILLA irin ta sauya jam\’iyyar siyasa ba ta irin Rt Honorabul Aminu Waziri Tambuwal zababben Gwamnan jihar Sakkwato ba ce, domin shi a fuskar al\’ummar jihar da ma kasa baki daya yana da kima da kwarjini da sanin ya kamata, sannan ga karbar shawara daga mutane ga kuma hangen nesa da uwa-uba tsoron Allah.
Farfesa Salisu Ahmed Yakasai na Jami’ar Usman Dan Fodio ne ya fadi haka yau Talata a yayin da yake amsa tambayar wakilinmu a ofishinsa da ke tsangayar Harsunan Najeriya da ke cikin jami’ar ta UDU a garin Sakkwato.
Farfesa Salisu Yakasai ya ce, ‘’ba ni bai wa Gwamna Tambuwal shawara ya bar jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyya, saboda a halin yanzu ne yake cikin ganiyar siyasarsa, kuma lokaci na zuwa da zai amsa kiraye-kirayen da ake yi masa nay a tsaya takarar shugaban kasar nan. Don haka ina mai shawartarsa day a ci gaba da jajircewarsa na hangen nesa tare da yin siyasa ta akida kamar irin ta magabatanmu su Shagari, Aminu Kano Awolowo da sauransu. Masu hankoron ya canza sheka ‘yan iza mai kantu ruwa ne’’.
Ya yi nuni da cewa, Gwamna Tambuwal a fagen aiki da sanin hakkokin ma’aikatansa ba a bar shi a baya ba, ka duba ayyuka da ya yi a jihar Sakkwato a bangarorin nomad a duk kayayyakin da noman ke bukata, wanda mafi akasarin al’ummar jihar manoma ne, ga kuma tsayuwa da ya yi irin na maid aka kan batun tsaro da ilmi da kiwon lafiya da jin dadi da walwalar ma’aikata da ma al’ummar jihar.
Farfesan wanda ya nusar da Gwamnan cewa ya kara hakuri Allah zai ida masa nufinsa cikin hukuncinSa inda komai nan gaba zai zo masa da sauki ganin Allah yana daga tauraruwar Tambuwal sannu-a-hankali har ya kais hi zuwa shugabancin kasar nan baki daya ga dukkan alamun da ake gani duk da su ba ‘yan siyasa ba ne.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here