Kwastan Ta Tara Fiye Da Naira Miliyan 78 Daga Yankin Arewa Maso Gabas

0
564
Rabo Haladu Daga Kaduna
HUKUMAR kwastan ta ce ta tara fiye da Naira miliyan 78 daga jihohin Borno da Yobe duk da rikicin da ake fuskanta.
Jihar Borno ita kadai ce jihar da ke makwabtaka da kasashen Afirka guda uku da suka hada
da Chadi, da Nijar da kuma Kamaru.
Baya ga matsalar rikicin Boko Haram, jihar na fuskantar sauran matsaloli musamman na fasa kwori da ya shafi dukkan makwabtan kasashen uku. Kwanturolan da ke kula da jihohin
Borno da Yobe, Mista Angbalaga Joshua ya bayyana cewa an rufe iyakoki guda 10 cikin guda 13 da ake da su a jihohin biyu sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro. A yanzu haka suna gudanar da kwarya-kwaryar ayyuka ne akan iyakokin da suke Gamboru, da Banki da
kuma Geidam.
A ranar 29 ga watan Yuni ne ya ce suka kama wata babbar mota dauke da shinkafar waje da kuma wake – wanda aka yi amfani da shi domin batar da sawu.
Kwanturolan ya yabi rundunar sojin Najeriya da ya ce da taimakonsu ne aka samu nasarar kame wadannan kayayyakin.
Kwanturolan Jihar Borno ya yi karin haske game da ayyukansu a wannan yankin, inda ya bayyana abubuwan da ba a haramta shigowa da su ba: kifi,wake, masara da kuma dabbobi
kamar shanu, awaki, tumaki da sauransu, wadanda kawai suke karbar kudin fito a kansu.
Sannan ya ce akwai umarnin da aka ba su na cewa duk abinda ya shafi abinci, ko daga ina ne idan kwastan ta kama, to a yi saurin kai wa \’yan gudun hijira.
Baya ga matsalar tsaro, kalubalen da suke fuskanta shine yadda hanyoyi ba sa biyuwa musamman a lokacin damina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here