Za Mu Yi Amfani Da Na\’urar Zamani – Mr La

0
649
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
DAN takarar kujerar Majalisar Dattawa daga mazabar tsakiyar Kafuna Alhaji Lawal Adamu Usman da ake wa lakabi da Mr La, ya bayyana kudirinsa na yin amfani da na\’urar zamani ta karamin jirgin da ke yawo a sama amma yana daukar hoto daga kasa.
Ita dai wannan na\’ura da ake kira Drums za a ganta tana yawo a sama amma kuma ta rika daukar hoton abin da ke kasa, Lawal Adamu Usman ya ce tuni ya sawo irin wannan karamin jirgin daukar hoto ko bidiyo mai motsi zai kuma rabawa kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomin da yake neman su zabe shi a matsayin Dan Majalisar Dattawa wato sanata.
Ya dai bayyana hakan ne a wajen wani taron da matasa Maza da mata daga daukacin kananan hukumomi Bakwai da zai wakilta a Majalisar da  suka taru a cikin garin Kaduna da suka Dade suna don yin Tozali da matashin Dan takarar na Majalisar Dattawa.
\”Wannan taari ne na zamani domin yin amfani da ci gaban da zamani ya kawo kuma yin hakan zai taimaka a wajen harkar tsaro, domin duk abin da Tawagar neman zabe take yi a kasa jama\’a a cikin wayoyinsu suna nan suna kallon duk abin da ke gudana\”. Inji Mr La.
Sai ya yi kira ga matasa da su kara zage damtse domin neman yancin kansu musamman ta fuskar darewa a kan Madafun IMO, inda ya fito fili ya shaidawa dimbin Matasa Maza da matan da suka taru a wajen wani taron gangamin tattaunawa da Dan takarar a karo na farko.
Kasancewa shi mulki ba bayar da shi ake yi ba sai dai matasa su tashi domin su karba, Wanda hakan ya zamarwa matasa wajibi saboda idan aka yi la\’akari da irin yadda al\’amura suke gudana a kasa za a ce tamkar an AJIYE matasa a gefe daya ne kawai.
Ya ci gaba da cewa shi a matsayinsa na da a wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari sai da ya gaya Masa wadansu abubuwa biyar a matsayin shawara da idan an dauki mataki wajen gyara su komai zai tafi dai dai a duk fadin Nijeriya.
\”Na farko shi ne na gaya Masa a dauki matakin gyara harkar Ilimi,Tsaro,Tattalin arzikin kasa, Samawa matasa aikin yi da kuma samar da isasshiya kuma ingantacciyar wutar lantarkin da masana\’antu za su yi aiki da ita, idan an samu wadannan a farko komai zai iya biyo wa baya amma a yanzu wane hali ake ciki Kowane matashi ya Tambayi kansa ya samu amsa don haka matasa a zage damtse ta yadda za a samu kyakkyawan canji\”.inji Mr La a Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here