Guguwar Canjin Sheka: Jam\’iyyar APC Za Ta Maka \’Yan Majalisarta Da Suka Fice Kotu

0
697

Daga Usman Nasidi
MAMBOBIN majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC sun yi watsi da batun canjin shekar da wasu daga cikinsu suka yi a jiya Talata.

Mambobin na APC, tab akin shugaban masu rinjaye a majalisar, Femi Gbajabiamila, sun sanar da cewar zasu dauki matakan shari’a a kan ‘yan mambobin da suka fice.

Kimanin mambobin majalisar ta wakilai 37 ne suka fita daga jam’iyyar APC mai mulki a yau, 33 sun canja sheka ne zuwa PDP yayin da wasu 4 daga jihar Osun suka koma sabuwar jam’iyyar ADC, ta tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Da yake Magana a madadin ragowar mambobin jam’iyyar APC a majalisar wakilai, Gbajabiamila, ya bayyana cewar canjin shekar abokan aikin nasu ya saba ka’ida.

“Babu rudani dangane da abinda suka aikata, sashe na 68 ya gama warware komai dangane da canjin shekar jam’iyyar dan majalisa. A saboda haka zamu bawa uwar jam’iyya karfin gwuiwar tafiya kotu domin daukan matakin day a dace a kan su,” a cewar Gbajabiamila.

Sannan ya cigaba da cewa, “Jama’a ne suka zabe su a karkashin tutar APC, kujerar mallakar jam’iyya ce, a saboda haka duk wanda ya bar jam’iyya ba zai tafi da abinda yake na jam’iyyar ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here