Majiyarmu ta samu labarin cewa Sanatan mai suna Rilwan Adesoji Akanbi ya bayyana haka ne a ranar Talata, 24 ga watan Yuli, inda ya karyata batun komawarsa PDP daga APC, kuma ya jaddada biyayyarsa ga APC, tare burin cigaba da zama a cikinta.
Sanatan Rilwan ya bayyana bacin ransa tare da kaduwarsa da yadda ya ji shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya ambaci sunansa a cikin Sanatocin da suka yi odabo da jam’iyyar APC ta baba Buhari.
“Babu yadda za’ayi na rusa gidan da na taimaka wajen gina shi, ni dan Buhari ne dari bisa dari, kuma Tinubu ne Maigidana, haka zalika gwamnan jihar Oyo Ajimobi gwamnanane, kuma Yayana, duk masu yunkurin bata min suna sun ji kunya.” Inji shi.
Daga karshe Sanata ya bada tabbacin cewa zai kira taron manema labaru da nay an jaridu don bayyana ma Duniya kin amincewarsa da fita daga jam’iyyar APC.