Rabo Haladu Daga Kaduna
SHAHARARREN dan kasuwar nan Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilan da suka sa ba zai iya rage farashin siminti ba, kamar yadda gwanatin tarayya ta nema.
A kwanakin baya ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bukaci Dangote da mai
kamfanin BUA Abdussamad Isyaku Rabiu su rage farashin siminti.
Dangoten ya kuma yi karin haske kan inda aka kwana dangane da aiki matatar mai da yake ginawa.
A tattaunawar da suka yi da manema labarai yana cewa an kusa kammala aikin matatar man