Yadda Wani Daraktan Makaranta Ya Yi Wa \’Yan Mata Fyade

0
1052
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A wani al\’amari mai like da ban takaici da ya faru a garin Abeokuta a tarayyar Nijeriya wadansu Dalibai ne sama da dari biyu suka yi taron manema labarai a Kaduna inda suka koka da irin yadda Daraktan Makarantarsu ya rika yin lalata da Yan yara kanana ba tare da la\’akari da kankantarsu ba.

Shugaban kungiyar na kasa Ado Nicodemus Baghibawa ne ya karanta wa manema labarai takardar kamar haka.

Ita dai wannan makaranta da ke garin Abeokuta mai suna cibiyar kasa da kasa ta S\’t Stephen da Rabaran Isaac Oluwole Newton Wusu, yake wa shugabanci daliban da suka kammala makarantar kuma aka ci zarafin su a matsayinsu na kananan yara sun shaidawa taron manema labarai a Kaduna cewa shi dai mutumin da ya kasance Malamin addinin kirista mai mukamin Rabaran ya yi amfani da kasancewarsu na Yan gudun hijira da suka samu mafaka a cibiyar yana lalata da Yan Mata ba da son ran su ba, su kuma yara Maza yana sa su aikin karfi da ya wuce kuma kamar yin Gini bayan an biya kudin da masu irin wannan sana\’ar za su yi aikin.

Shi dai wannan dimbin zargi ya fito ne daga ainihin wata kungiyar da tsofaffin Dalibai suka kafa mai suna Concerned Past Students Of Stephen\’s Children Home (COPASSTECH), da ke da matsugunnin a Abeokuta Jihar Ogun a wajen wani taron manema labarai a Kaduna.

A wajen taron manema labarai daliban sun karanta jawabinsu kamar haka \” muna matukar farin cikin shaida maku cewa lallai hakika an ci zarafinmu ta hanyar cutar da mu wajen yin aikin karfi kamar na yin Gini a wannan makaranta da kuma yin lalata da wasu daga cikin yara Yan Mata da suke a wannan cibiya kuma mai wannan aiki shi ne Rabaran Isaac Oluwole Newton Wusu, da ya kasance mai kula da wannan cibiya amma ya rika karya mana yancin mu na zama Yan kasa Kuma mutane masu yanci don kawai muna zaune a wannan cibiya ta kasa da kasa.

\"\"

\” A alkalumman da muke da shi a halin yanzu akwai Dalibai Yan Mata 20 da aka yi lalata da su kuma Wanda ake zargi Daraktan cibiyar ne ya aikata hakan\”.

Suka ci gaba da cewa Babu shakka akwai wadansu daga cikin su na tare da mu kuma sun amince su yi bayani a kan abin da ya faru a wannan cibiya.

A gefe daya Kuma Dalibai Maza an rika sanya su aikin karfi kamar idan za a yi Gini a makarantar bayan Kuma an biya kudin komai na aikin

Muna sane da akwai wadansu da suke taimakawa cibiyar daga kasashen waje duk sun biya komai na aikin amma sai a rika kusa mu dole muna yin aikin

Suka ce akwai lokacin da aka Kai maganar kotu amma daga baya sai kawai aka wallafa a wata jaridar kasar cewa an Kori karar ba tare da yin wata shari\’a ba.

\”Don haka a matsayinmu na Wanda abin ya shafa muna kira ga Gwamnatocin Jihohin Kaduna,Borno,Yobe,Adamawa,Nasarawa da Filato da su tashi tsaye domin Nemo mana yancin mu a hannun wannan mutum, kasancewar daman duk mun fito daga Arewacin Nijeriya ne saboda duk jihohin da ake fadace fadace ne ake daukar yayansu da sunan za a Tallafa Wa yaran suyi karatu amma sai mu buge da irin shiga irin wannan halin\”. Inji daliban ta bakin shugaban kungiyar tasu na kasa Ado Necodemus Baghibawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here