Daga Usman Nasidi
A RANAR Juma\’a ne wasu \’yan fashi da makami suka kashe wata budurwa mai suna Njoku Uchechi a wata fashi da suka yi kusa da Diamond Bank dake Suru-Alaba dake Legas.
\’Yan fashin sun tare ta bayan ta fito daga bankin sannan suka harbe ta a kai. Sun kuma yi awom gaba da zunzurutun kudi N150,000 data ciro daga bankin
Sai dai wasu mutane dake wucewa ta hanyar sun yi nasarar kama daya daga cikin \’yan fashin yayin da daya dan fashi ya tsere da kudaden.
Bayan kama shi, mutane sunyi masa duka har ya kasa motsawa sannan suka dauko tayoyin mota suka makala masa suka banka masa wuta.
An kone daya daga cikin \’yan fashin da suka kashe wata kyakykyawar budurwa, duba hoto An kone daya daga cikin \’yan fashin da suka kashe wata kyakykyawar budurwa, duba hoto
Tuni dai an kai gawar marigayiyar dakin ajiye gawarwaki na asbiti. Mutane da dama sun yi jaje game da rasuwar budurwar wanda haka siddan \’yan fashin suka tare ta kuma suka halaka ta.