Kwankwaso Ko Mazabarsa Ba Zai Iya Kawowa Ba — Ganduje

    0
    785
    Gwamna Ganduje Na Jihar Kano
    Rabo Haladu Daga Kaduna
    GWAMNAN Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ba zai iya lashe zabe a mazabarsa ba, ballantana ya iya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari.
    Gwamna Ganduje ya fadi haka ne yayin da aka ruwaito Kwankwason na ikirarin zai iya kayar da Shugaba Buhari idan PDP ta tsayar da shi takara.
    \”Maganar Kwankwaso na nuna cewa ya zama rudadden dan siyasa wanda ke kama duk wata dama da ta zo masa domin ya dawo da matsayinsa a siyasance.
    \”Sama da shekara uku yana Majalisar Dattawa yana barci ba tare da ya gabatar da kudurin da zai amfani mutanen Najeriya ba,\” a cewar
    Ganduje, wanda tsohon na hannun   daman sane. Ganduje ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Kwaminishan Yada Labarai na jihar, Muhammad Garba ya sanya wa hannu.
    Sanarwar ta kara da cewa: \”Sama da shekara uku da ya yi a majalisar, bai ziyarci mazabarsa ba, ka na bai yi musu wani aikin a zo a gani ba.\” \’Ni ne na fi kowa cancantar yi wa jam\’iyyar PDP takara\’
    Tsohon gwanman Kano kuma Sanata a jam\’iyyar APC ya ce shi ne mutumin da ya fi kowa karfi da farin jinin da zai iya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019. Injiniya Rab\’iu Musa Kwankwaso ya shaida wa fitaccen dan jaridar kuma mawallafi, Dele Momodou shi yanzu ba shi da wata jam\’iyya amma PDP ce ta fi kowacce dama da karfin kayar da shugaban, idan har ta ci gaba da bin tafarkin demokuradiyya.
    \”PDP na bukatar tsayar da mutumin da ya fito daga jihohin Kano, Katsina ko Kaduna takarar shugaban kasa idan har tana son yin nasara domin su ne jihohin da suka fi ko\’ina yawan kuri\’u,\” in ji shi. Sannan ya ce shi ne ya fi kowa \”cancantar yi wa jam\’iyyar takara\”.
    Tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar, wanda dan jihar Adamawa ne, da tsohon
    gwamnan Jigawa Sule Lamido, da na Kaduna Ahmed Makarfi, da na Kano Malam Ibrahim
    Shekarau na cikin wadanda suka bayyana aniyarsu ta neman takara a PDP.
    Sai dai a kwanakin baya Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai kuma na hannun damar Shugaba Buhari, ya ce Kwankwaso ba zai iya hana Buhari lashe zabe a Kano ba a badi.
    Kalaman na Kwankwaso na zuwa ne \’yan kwanaki bayan ya kauracewa babban taron
    jam\’iyyar APC na kasa, yana mai cewa an nuna ba a yi da shi.
    Sanatan na cikin shugabannin bangaren tsaffin \’yan PDP wanda ya kunshi Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, da na Wakilai Yakubu Dogara, da suka yi zargin ana muzguna musu a APC kuma gwamnatin Buhari ta mai da su saniyar-ware. Zargin da jam\’iyyar da gwamnatin suka musanta, kuma an fara tattaunawa domin duba korafe-
    korafen nasu.
    Wannan ita ce alama mafi girma da kawo yanzu ta nuna inda jagoran na Kwankwasiyya, wanda ya dade yana rigima da tsohon mataimakinsa kuma mutumin da ya gaje shi a gwamnan Kano,
    Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya nufa. Domin ya nuna cewa zai iya komawa jam\’iyyar
    PDP idan har za a bi tafarkin dimokuradiyya wurin fitar da dan takarar shugaban kasa.
    Sai dai masana na ganin kalaman na tsohon gwamnan da kuma take-takensa a baya-bayan nan sun nuna cewa tuni ya riga ya yanke wa kansa hukunci.
    A makon da ya gabata ne aka rawaito cewa ya yi wata ganawar sirri da tsohon mataimakin
    shugaban kasa Atiku Abubakar a Abuja, sannan ya ziyarci jihar Ekiti don tattaunawa da GwamnaAyo Fayose, inda kuma ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar PDP a zaben gwamman jihar da za a yi nan gaba a wannan watan.
    Idan har Kwankwaso ya fice daga APC, to zai zamo dan siyasa mafi girma da ya bar jam\’iyyar tun bayan ficewar Atiku Abubakar a watan Nuwamban bara

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here