Daga Usman Nasidi
Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta shirya tsaf domin kafa sabbin ma\’aikatu guda biyu a karkashin babbar ma\’akatar dake kula da kimiyya da fasaha watau (Ministry of Science and Technology) a turance.
Mai\’aikatun da za\’a kafa din dai sune na kwararowar hamada da zaizayar kasa da kuma bincike watau (National Agency for Desertification & Erosion Research NADER) da kuma ta na\’urorin zamani watau (Research in Robotics & Artificial Intelligence NARRAI).
A wani labarin kuma, Tsohon shugaban babban bankin tarayyar Najeriya kuma Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi ya caccaki gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari da kasar Afirka ta kudu bisa kan kin rattaba hannu akan yarjejeniyar kasuwanci a Nahiyar Afirka.
Sarkin ya ce abun takaici ne ace kasashen Afirka 44 duka sun sanya hannu a takardar amma Najeriya da Afirka ta Kudu sun kekashe kasa sun kiya inda yace ya kamata a sake zama domin lalubo bakin zaren.