Rabo Haladu Daga Kaduna
\’YAN majalisar dokokin jihar Kano sun tsige Shugaban Majalisar jihar Alhaji Yusuf Abdullahi Ata, bayan da aka shafe tsawon lokaci suna kokarin yin hakan.
A ranar Litinin da safe ne \’yan majalisar 27 daga cikin 40 suka sanya hannu a kan kudurin tsige Honorabul Ata, ciki har da shugaban marasa rinjaye daya tilo da ke majalisar.
A watan Mayun da ya gabata dai jami\’an \’yan sanda sun yi wa majalisar kawanya, don hana \’yan majalisar shiga a kokarinsu na tsige shugaban.
\’Yan majalisar dai na zargin kakakin nasu da rashin iya gudanar da aiki, da raba kawunan \’yan majalisar da kuma zubar da kimar majalisar a idon al\’umma. Sai dai ya musanta aikata wannan laifin tun a lokacin.
A yanzu dai \’yan majalisar sun nada tsohon kakakin Kabiru Alhassan Rurum, wanda ya yi murabus a watan Yulin bara, bisa zargin sa da aikata wasu laifuka da suka shafi cin hanci.