Babban Sufetan \’Yan sanda Ya \’Daga Dan sandan Dake Tafsirin Al-Qur’ani Zuwa Mukamin Kwamishin

0
696

 

Daga Usman Nasidi

BABBAN sufetan Yan sandan Najeriya ya amince da nadin Ahmad Abdulrahman a matsayin sabon kwamishinan Yan sandan jihar Kaduna,

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, kuma hadimin gwamnan jihar Kaduna, Malam Hayatuddeen Lawal Makarfi ne ya bayyana haka a shafinsa.

Sabon Kwamishina yan sandan Ahmad ya kasance yana gudanar Tafsirin Al’Qur’ani a duk watan Azumin Ramadan a babban Masallaci dake shelkwatar rundunar Yan sandan jihar Kaduna, inda yake fassara Al’Qur’ani da ilimi iya gwargwado.

A wani hira da aka taba yi da Ahmad, yace babban dalilin shigarsa aikin Dan sanda shi ne tun bayan wani rikici da aka taba yi na Zangon Kataf a jihar Kaduna, inda yace Sojoji suka kama su ana wannan rikicn, basu sake su ba har sai da mariyagi Malam Abubakar Mahmud Gumi ya kwace su da kyar.

Ahmad ya ce bayan Malam ya kwace su ne sai yake basu shawarar su shiga aikin Soja da Dan sanda don su kare mutuncin addinin su, inda ya jaddada musu cewa inda akwai nasu a cikin aikin ba za’a dinga ci musu mutunci ba, wanda hakan ne yasa shi yanke shawarar shiga aikin Dan sanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here