EFCC Na Zargin Gwamnan Benue Da Wawure Kudade Akalla Naira Biliyan 22

0
560

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

HUKUMAR EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta\’annati ta alakanta gwamnan jihar Binuwe Samuel Ortom, da yin sama da fadi da naira biliyan 22.

Hukumar ta kuma ce ana kan bincikar \’yan majalisar jihar 21 kan zargin juya akalar naira miliyan 375 da ya kamata su yi amfani da su wajen sayen motoci.

Gwamna Ortom bai mayar da martani ba game da zargin wanda ke cikin wani rahoton binciken da aka fara a shekarar 2016.

Rahoton ya nuna cewa gwamnan ya sa an cire naira biliyan 21.3 daga asusun gwamnati tsakanin ranar 30 ga watan Yunin 2015 zuwa watan Maris na 2018.

A rubuce dai, ya kamata kimanin naira biliyan 19 daga cikin kudin ya zama kudin biyan hukumomin rundunar tsaro shida da aka tura jihar, domin dakile hare-hare tsakanin makiyaya da manoma ne.

Sai dai kuma, EFCC ta ce an biya hukumomin tsaron kasa da naira biliyan uku daga cikin kudin, kuma babu wanda ya san yadda aka yi da sauran kudin.

A ranar 25 ga watan Yuli ne Gwamna Ortom ya sanar da ficewarsa daga jam\’iyya mai mulki ta APC zuwa jam\’iyyar adawa ta PDP.

Gwamnan ya sauya shekar ne tare da wadansu shugabannin kananan hukumomin jihar 14. Jam\’iyyar APC dai ta ce ta yi mamakin sauya shekar Mista Ortom din daga jam\’iyyar zuwa PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here