Daga Usman Nasidi
A RANAR Talata ne Manjo Janar Abba Dikko ya karbi ragamar jagorancin rundunar dakarun soji ta Ofireshon Lafiya Dole dake aikin kakkabe ‘yan kungiyar Boko Haram da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Dikko ya karbi jagorancin rundunar ne daga hannun abokin aikinsa Manjo Janar Rogers Nicholas, wanda aka nada a watan Disamba na shekarar 2017. Nicholas ya mika jagoranci ga Dikko a wata cibiya dake sansanin soji a garin Maidugurin jihar Borno.
Nicholas ya yi kira ga sabon kwamandan daya dora a kan nasarorin da ya tarar an samu a kan mayakan kungiyar Boko Haram.
Manjo Janar Abba Dikko ya maye gurbin Rogers Nicholas hakazalika ya yi godiyar ga rundunar sojoji dake jihar Borno bisa goyon bayan da suka bashi lokacin da yake jagorantar su.
A wani labarin kuma, rahotanni na bayyana cewar rundunar soji dake aikin mayar da martani cikin gaggawa (Quick Response Force) tayi nasarar cafke wasu \’yan fashi da makami a Felele dake kan hanyar Lokoja zuwa Okene.