Daga Usman Nasidi
LABARIN da ke shigowa yanzu da dumi-dumi na nuna cewa bayan rikice-rikice, zanga-zanga da fadan baki, shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya sanar da fitarsa daga jam\’iyyar APC.
Shugaban majalisan ya yi wannan sanarwa ne da yammacin ranar Talata ta shafin sada ra\’ayi da zumuntarsa na Tuwita. A jawabin da ya yi yace: \” Ina son sanar da ‘yan Najeriya cewa bayan shawarwarin da nayi sosai, na yanke shawaran fita daga jam\’iyyar All Progressives Cogress APC.\”
Wannan lamarin na faruwa ne bayan wasu daruruwan matasa sun tafi zanga-zanga sakatariyan jam\’iyyar APC da ke babban birnin tarayya Abuja.
Sanatan Bukola Saraki ya zayyana wasu dalilai akalla bakwai da ya ce sune musabbabin ficewar sa jam\’iyyar. inda ya ce “ na farko ya fahimci cewa wasu \’yan jam\’iyyar basu son zaman lafiya ba kuma su ba kowa darajar sa.
Na biyu ya ce haka ma dukkan wasu ginshikan da aka kafa jam\’iyyar da su anyi fatali da su, na uku ana cigaba da muzgunawa abokan siyasar sa a cikin jam\’iyyar tamkar wasu bare marasa gata ko \’yanci. Abu na hudu shi ne wasu tsiraru a jam\’iyyar sun hana duk wani yunkurin da ya yi domin ganin an samu daidaito.
Na biyar ita ce gwamnatin tarayya kuma ba ta baiwa yan majalisu darajar su. Na shida ana yiwa duk wanda ya so kawo gyara ko bayar da shawara kudin goro da cewa ya saci kudin gwamnati ne. Sannan abu na karshe shi ne gwamnatin APC din tana nema ta mayar da majalisar tarayya \’yan amshin shata kawai.
An fara samu baraka a jam\’iyyar APC ne tun ranar Talatan da ya gabata, 24 ga watan Yuli, 2018 inda wasu ‘ yan majalisan dattawa akalla 15 suka fita daga jam\’iyyar APC da ‘yan majalisan wakilar 35.
Abin mamakin shi ne Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara da shugaban majalisan, Bukola Saraki, sun zauna a jam\’iyyar.
Masu sharhi sun bayyana cewa akwai wani kaidi da suke shirin kullawa da wannan rashin fita da sukayi.