Rabo Haladu Daga Kaduna
TSOHON Gwamnan jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce kaddara ce ta fada wa Tambuwal bayan ya fita daga APC.
Sanata Wamakko ya shaida wa manema labarai cewa yana nan a cikin jam\’iyyar APC daram dam ba abin da zai fitar da shi, yana mai cewa \”jama\’ar Sakkwato Alu suke da Buhari\”, sabanin tunanin da ake shi ma yana kan hanyar fita daga APC.
\”Siyasa wata abu ce da mutane ke cewa gaba da kallo baya da mamaki.\” Duk wanda ya san yadda siyasar Sakkwato take, don an ce ma sa wani mutum ya fita jam\’iyyar
da Alu yake ciki kuma Buhari yake ci to zai ce
wata kaddara ce tafada masa.
Ana ganin fitar Gwamna Tambuwal daga APC ya nuna akwai matsaloli da jam\’iyyar ke fama da su a Sakkwato musamman tsakanin shi da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko wanda ya gada kuma ake ma sa kallon mai gidansa.Ko ya ce fitar Tambuwal daga APC \”abin
tausayi ne ga yaro matashi irinsa da ke gaggawa a harakar rayuwa.\”
\”Tun tuni jama\’ar Sakkwato sun daina yin jam\’iyya domin su mutum suke yi. Saboda haka idan mutum ya fito ya ce ya bar Buhari ya bar Alu to sai ya zama abin mamaki da ban tausayi.\”
Har ila yau, Wamakko ya yi ikirarin cewa jam\’iyyar APC ce za ta kafa gwamnati a Sakkwato
kuma Buhari ne zai lashe zabe a jihar.
Ya ce ya fice PDP ne saboda yin biris da shawarwarin da suka bayar na bukatar gyara a
jam\’iyyar, bayan an tambaye shi kan yadda takwarorinsa na sabuwar PDP ke fita suna komawa inda suka fito.
\”Idan har ina da wani korafi ko bukatar gyara a APC, fita daga jam\’iyyar ba uzuri ba ne kuma ba shi zai nuna mutum ya san abin da yake ba.\” \”Ka tsaya ka fadi a fadi, ka ja, a ja har a gano gaskiya a yi aiki da ita, mutanen da nake wakilta a Sakkwato ra\’ayinsu APC da Buhari kuma ra\’ayinsu Alu don haka ba zan saba wa mutane na ba.\” inji Alu.