Babu Wanda Zai Kara Fita aga APC Cikin Gwamnoni 22 Da Muke Da Su – Gwamnonin APC

  0
  738

   

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  SHUGABAN Kungiyar Gwamnonin jam\’iyyar APC Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya ce babu wani da zai kara fita daga jam\’iyyar.

  Gwamnan ya ba da wannan tabbacin ne lokacin da yake magana da manema labarai bayan wata ganawa da gwamnonin jam\’iyyar suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.

  Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da wadansu gwamnoni uku ne a baya-bayan nan suka sauya sheka daga jam\’iyyar zuwa jam\’iyyar
  adawa ta PDP.

  Amma gwamnonin APC 22 sun bai wa Shugaba Buhari da kuma Shugaban jam\’iyyar Adams Oshiomhole tabbacin samun nasara a zaben shekarar 2019 a jihohinsu.

  \”Har yanzu muna da karfi kuma kawunanmu a hade suke. Muna da iko a jihohi 22 da sanatoci 53. Har yanzu mu ne ke da rinjaye. Kuma muna fatan samun karin jama\’a a jam\’iyyarmu,\” in ji Gwamna Rochas.

  Ya ci gaba da cewa \”Mun bai wa shugaban kasa tabbacin cewa muna tare da shi. Kuma babu wani mutum da zai kara fita jam\’iyyar. Muna ba \’yan Najeriya tabbacin cewa mu ne za mu sake yin nasara a zaben shekarar 2019.\”

  An yi ganawar ce gabanin hutun kwana 10 da shugaban zai fara a ranar Juma\’a a birnin
  Landan.

  Shugaban ya yi ganawar ne sa\’o\’i kadan bayan Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal ya sanar da koma wa jam\’iyyar PDP daga APC, wato ya bi sahun takwarorinsa na jihohin Kwara da Benue.

  Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka zuwa yanzu
  sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, Kakakin jam\’iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed, Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu Ahmed Ibeto, Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, \’Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif.

  Hakazalika, gamawa da sauran su bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa\’i bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 – wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam\’iyyar Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam\’iyyar ADC.

  Hakeem Baba Ahmed – shugaban ma\’aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Usman Bawa – mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here