Dalilin Da Ya Sa Saudiyya Ta Rage Adadin Mahajjatan Najeriya.

0
655

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

.
A BANA maniyata 50,000 ne za su yi aikin Hajjin bana, sabanin dubu chasa\’in da
biyar, kuma tuni har an riga an kwashe alhazai dubu goma sha daya da dari hudu, wadanda a bana suna sauka a birnin Madina ne kai tsaye.

Shugaban hukumar Alhazai na kasa, Barista Abdullahi Muktahar, ya ce rage yawan alhazan da aka yi, ya biyo bayan wani matakin aiki ne da hukumomin Saudiyya suka gindaya.

Daga cikin ka\’idojin da suka gindaya, hukumomin na Saudiyya sun ce sun dauki wannan mataki ne domin sanin yawan bakin da za su je kasar don yi musu tanadi.

Sai dai kuma a Najeriya, bayanai sun nuna cewa sai makonnin biyun karshe da za a rufe filin jirgin sama ne wasu mutane ke biyan kudinsu na zuwa Makka.

Barista Abdullahi ya yi kira ga masu kula da ayyukan hajji da masu ruwa da tsaki, da cewa ka da su bari masu suka su karkatar da hankalinsu.

Ya kara da cewa bin ka’idoji da
dokokin da aka gindaya, musamman don gudanar da ayyuka cikin nasara, na da matukar muhimmanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here