Ganduje Yana Min Azaba – Mataimakin Gwamnan Kano

0
644

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

MATAIMAKIN gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya yi zargin cewa yana fuskantar cunzgunawa daga abokin aikinsa Gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Farfesa Hafiz ya ce sama da shekara biyu ke nan gwamnatin Kano ta mayar da shi saniyar ware tare da hana shi hakkokinsa, saboda yana biyayya ga Sanata Rabi\’u Musa Kwankwaso.

Farfesa Hafiz ya bayyana cewa rayuwarsa na cikin hadari, yana mai bada misali da abinda ya faru ga wani jami\’in gwamnatin Kano Dr. Bala
Muhammad a 1981, inda aka bi shi har gida aka kashe shi, yayin wata zanga-zangar kin jiningwamnatin Abubakar Rimi.

Mataimakin na gwamnan Kano ya ce da kudinsa ya ke yi wa gwamnatin Kano duk wata hidima daya ke yi mata.

Ya yi zargin cewa duk abinda ake yi masa ana yi masa saboda alakarsa da Kwankwaso. Akwai mummunar hamayyar siyasa tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Ya ce kawo yanzu yana nan a cikin jam\’iyyar APC kuma har yanzu shi ne mataimakin gwamnan jihar Kano. To amma fa ya ce ya daure kayansa domin ficewa daga jam\’iyyar ta APC idan lokaci ya yi.

Har yanzu gwamnatin Kano ba ta mayar da martani kan zarge-zargen da Farfesa Hafiz Abubakar ya yi ba, amma dai manema labarai na ci gaba da tuntubar gwamnatin don jin martaninta.

A farkon wannan makon dai gwamnatin ta Kano ta musanta cewa mataimakin gwamnan yana fuskantar wata barazana, sannan kuma babu wani shiri na tsige shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here