Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
SANANNEN mawakin nan mai kokarin fadakar wa game da al\’amuran duniya har ma da gargadi a kan ranar kiyama Malam Yahaya Makaho, ya bayyana cewa ya kaddamar da wakokinsa ne domin samun abin da zai taimaka wa \’yan uwa masu bukata ta musamman da ake wa lakabi da nakasassu.
Malam Yahaya Makaho, ya dai bayyana hakan ne a dakin taro na dandalin tunawa da Murtala da ke Kaduna, inda ya ce yana son ne ya himmatu domin fadakar da \’yan uwa masu bukatar musamman ta wajen koyar da su sana\’o\’i, ilimin addini da na boko domin su fahimci ba wai barace-barace ba ne kawai abin yi ba a rayuwa, kasancewar rayuwa da fadi don haka akwai bukatar a fadakar da \’yan uwa cewa nakasa ba karshen rayuwa ba kenan.
\”Na yi wannan taron kaddamar wa ne domin nima in yi wa wadansu irin abin da aka yi mini har na kawo kamar yadda nake a halin yanzu, a kwanan baya an yi taron kaddamar da wakata a garin Abuja an Tara kudi masu yawa kuma an yi amfani da su aka daya mini gidan da nake ciki a yanzu, wannan abu hakika ya sa ni canza tunani ta yadda zai kafa wata gidauniyar taimakawa \’yan uwa masu bukata ta musamman\”.inji Yahaya
Ya kuma ci gaba da cewa akwai wani tsarin kuma na kafa wata makarantar koyar da masu bukata ta musamman yadda za su koyi sana\’o\’i za kuma a rika yin amfani da abin da aka koya wa daliban a sayar a kasuwa ta yadda a haka za a samu damar rike makarantar ta hanyar samar da kayayyakin koyarwa da biyan malamai kudin su.
\”Hakika mun zagaya wuraren da masu bukatar musamman suke mun kuma ga abubuwan ban tausayin da suka sa dole mu tashi tsaye domin ganin an taimaka wa juna baki daya\”.
A wajen taron kaddamar da wannan wakar domin kafa gidauniyar an ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Dakta Muktar Ramalan Yero, Alhaji Yaro Makama Rigachikun, wakilan Gwamnatin Jihar Kaduna da Dakta Hakeem Baba Ahmad da kuma masu sana\’ar fina-finai da wakokin Hausa da Turanci irin su Aminu Alan Waka, Hadiza Gabon, sarauniyar Kannywood da sauransu, taron dai ya kayatar an kuma yi an tashi lafiya.