Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
YAYAN jam\’iyyar APC na gaskiya da suka fito daga mazaba ta shida a Unguwar Tudun wada ta karamar hukumar Kaduna ta kudu sun kara jaddada tabbacin ana tare tsakaninsu da sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da Abbas Muhammad Anni shugaban mazaba ta shida ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a kaduna.
\”Hakika muna tare da sanata Shehu Sani don haka muke jaddada cikakken Goyon bayan mu a gare shi\”.
Takardar dai ta ci gaba da cewa biyo bayan irin yadda aka ankarar da ainihin shugabannin APC na mazaba ta shida da suke a Unguwar Tudun wada musamman a kan irin yadda al\’amura siyasa suke tafiya a halin yanzu, Wanda wadansu Yan Loren wani mutum suke yi na cewa wai \”har yanzu sun jaddada irin korar haramcin da suke yada wa tun kwanan baya a kan dakatar da sanata mai wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya Shehu Sani daga jam\’iyyar APC\”.
Inda takardar ta ci gaba da cewa duk wannan aiki ne irin na rashin hankali da Tunani mai kyau da wadansu masu neman Dan abin kashim Miya kawai suke yandarar kawunansu da shi.
Domin kamar yadda kowa ya Sani wutsiyar Rauni ta yi nisa da kasa wannan yasa tun da Dade wa bamu kula da irin wannan Yan neman kashim Mika da suke kokarin haifar da rudani a cikin jam\’iyyar APC.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa hakan yasa suke kara yin kira tare da fadakar wa ga yayan jam\’iyyar da kuma dukkan al\’ummar baki daya da su rika yin watsi da abin da Yan mini ka sha miyar siyasa ke kokarin yadawa.
Don haka, muna kara jawo hankalin yayan APC daga mazaba ta shida da sauran jama\’a cewa da su watsi da wannan ikirari na Dakatarwar da Yan tsiraru ke cewa su yi wa domin ba su da wata hujja ko madogara.
Saboda haka shugabannin a mazaba ta shida suke tabbatar da cikakken hadin Kai da Goyon bayansu ga Santa Shehu Sani domin hakan zai bashi damar samun ci gaba da yin Wakilci a zaben shekara ta 2019 idan zabe yazo da ikon Allah.
A tsawon sama da shekaru uku da Sanatan ya yi yana gudanar da Wakilci ya kawo kudirori da kuma yin ayyuka a duk inda ya samu kansa a cikin wani kwamiti ko aikin Majalisar Dattawa hakika hakan ya Isa Wakilci nagari, da samu martaba da mutunci a idanun jama\’ar kasa baki daya.
Takardar da Abbas Anni, ya sanya wa hannu ta ci gaba da cewa suna kyautata zaton cewa irin wannan matsalar da kalamai barkatai na kokarin yin Narayana ba su rasa nasaba da irin yadda shugaba Muhammadu Buhari ya daga hannun sanata Shehu Sani domin ya zama Dan takara a zaben 2019, Wanda hakan ya tayar da hankalin wani Dan takara daga gidan Gwamnatin Jihar Kaduna da ake zargin sa da kitsa dukkan wannan batu na Dakatarwar baki daya.
Kuma wannan batun Dakatarwar na yin nuni ne da irin yadda wadansu ke ci da zuciyarsu a wajen batun neman mukami musamman tsayawa zabe a APC, da suke kara ingiza Yan kanzaginsu su haifar da hatsaniya a jam\’iyya Wanda hakan ka iya haifar da matsala a damar lashe zabe da APC ke da shi a 2019.
Don haka kamar yadda takardar ta bayyana cewa shugabannin mazaba ta shida na kira ga shugabancin APC na kasa da kuma na Jiha dasu tsawatawa wadannan masu kokarin yin batanci ta hanyar yin aiki da dokar da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin APC.