SHUGABAN Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki zai yi zaman gaggawa da sauran shugabannin majalisar dokokin kasar a ofishinsa da ke Abuja ranar Talata.
Wani na kusa da shugaban majalisar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ne ya shaida wa manema labarai hakan.
Ya ce za a yi zaman ne tsakanin shugabannin majalisar dattawan da na wakilai kuma za su kwashe tsawon sa\’a guda suna tattaunawar.
Ya ce cikin batutuwan da za su tattauna har da batun zaben shekarar 2019, da batun sauya shekar wasu \’yan majalisar kasar.
Sai dai sabanin yadda wasu rahotanni suka bayyana, zaman ba zai duba batun tsige Sanata Saraki daga shugabancin majalisar ba.
\”Wannan ba ya daga cikin batutuwan da za su tattauna,\” a cewarsa majiyar mu.
A karshen watan jiya ne majalisar ta tafi dogon hutu bayan sauya shekar wasu \’yan majalisa fiye da 50 daga jam\’iyyar APC mai mulki zuwa PDP.
Akwai wasu rahotanni wadanda ba a tabbatar ba da ke cewa akwai wani shirin tsige Sanata Saraki daga kujerarsa, bayan da shi ma ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a makon jiya.