Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin \’Yan NYSC 9 A Taraba

0
623
Rabo Haladu Daga Kaduna
\’YAN sanda a jihar Taraba  sun tabbatar da mutuwar akalla masu yi wa kasa hidima (NYSC), tara, sakamokon tafiyar da ruwa ya yi da su ranar Asabar a kauyen Mayo Salbe da ke karamar hukumar Gashaka.
\’Yan sandan sun tabbatar wa da manema labarai  cewa zuwa yanzu sun gano gawawwakin bakwai daga cikin matasan, yayin da ake ci gaba a neman sauran biyun.
Bayanai sun ce matasan su fiye da 20 ne suka je yawon shakatawa ne a wani kogi amma sai kogin da ya ciko, ya yi awon gaba da wasu a cikinsu   hukumar \’yan sanda ta jihar Taraba David Misal, ya ce, matasan ba su yi aune ba sai kogin ya ciko ya makare, har ya yi
awon gaba da wasu daga cikin masu yi wa kasa hidimar.
Kogin Mayo-Selbe dai yana samun ruwansa ne daga babban Kogin Binuwai.
Mista Misal ya ce: \”Matasan suna cikin walwala da nishadinsu ne a kogin, to da alama an yi
ruwan sama a wani waje nesa kadan kuma ta wannan kogin yake ratsawa, sai ruwan ya taho da karfi ya tafi da tara daga cikinsu.\”
Ya kara da cewa a yanzu dai suna ci gaba da tantance jinsin gawawwakin don gano sunayensu da garuruwan da suka fito.
Wata matashiya daga cikin \’yan bautar kasar da take cikin tawagar da wadanda abin ya rutsa da su, ta ce: \”Sun isa wajen da karfe biyun ranar Asabar, kuma sai abokan tafiyarsu suka ce su je sashen da ya fi kayatarwa.\”
\”A kan hanyarmu ta dawowa daga bangaren da ya fi kayatarwar ne sai muka ga kogin ya ciko har yana ambaliya, sai kuma ruwan ya tafi da mutum tara daga cikinmu,\” a cewarta.
Rundunar \’yan sandan jihar dai ta ce yawancin wadanda abin ya rutsa da su \’yan kudancin
Najeriyar ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here