An Nada Sabon Shugaban Hukumar DSS

0
627
I G Na \'Yan Sandan Najeriya
Rabo Haladu Daga Kaduna
MUKADDASHIN shugaban NASA  Yemi Osinbajo ya umarci mutumin da ya fi mukami a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Matthew B. Seiyefa ya maye gurbin Lawal Daura, wanda aka sallama daga aiki ranar Talata.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da gwamnati  ta fitar ta shafinta na Twitter.
Hakazalika rahotanni suna cewa mukaddashin shugaban yana ganawa da sabon shugaban hukumar.
Rahotanni sun ce, Mista Seiyefa, mutumin da ya fito daga jihar Bayelsa, ya isa fadar shugaban kasar ne da misalin karfe 4 na yamma rike da wasu takardu a hannunsa.
A ranar Juma\’ar da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya fara hutun kwana 10 a
kasar Birtaniya.
Abin da ya sa mataimakinsa yake jan ragamar kasar a matsayin mukaddashin shugaba.
Matakin cire Lawal Daura din ya zo bayan wasu jami\’an hukumar DSS din sun hana wasu
Sanatoci shiga majalisar dokokin ta kasa  da safiyar Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here