Rabo Haladu Daga Kaduna
JAMI\’AN tsaron na farin kaya (DSS) sun hana wasu \’yan majalisar dattawa shiga
zauren majalisar da safiyar Talata.
Jami\’an, da suka ce sun tare hanyar shiga zauren ne bisa umarnin da aka ba su \’daga
sama\’, sun kyale \’yan majalisar sun shiga zauren majalisar daga baya.
Rahotanni dai suna zargin cewar hana \’yan majalisar shiga na da alaka da yunkurin tsige
shugaban majalisar, Bukola Saraki.
Wannan lamarin ya auku ne a lokacin da ake ci- gaba da takun-saka tsakanin shugaban majalisar da wadanda ke son tsige shi.
Wasu \’yan majalisar dake jam\’iyyar APC suna ganin ya kamata Saraki ya yi murabus daga
mukaminsa tun da dai ya fice daga jam\’iyyar APC mai mulki.
Sai dai kuma wasu \’yan jam\’iyyar PDP suna ganin bai kamata Saraki ya sauka daga
mukaminsa ba.
A ranar Litinin ne Shugaban Majalisar Dattawan Bukola Saraki ya sanar da cewa zai yi
zaman gaggawa da sauran shugabannin majalisar dokokin a ofishinsa da ke Abuja
ranar Talata.
Wani na kusa da shugaban majalisar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ne ya shaida wa manema labarai hakan.
Ya ce za a yi zaman ne tsakanin shugabannin majalisar dattawan da na wakilai kuma za su
kwashe tsawon sa\’a guda suna tattaunawar.
Ya ce cikin batutuwan da za su tattauna har da batun zaben shekarar 2019, da batun sauya shekar wasu \’yan majalisar
Sai dai sabanin yadda wasu rahotanni suka bayyana, zaman ba zai duba batun tsige Sanata Saraki daga shugabancin majalisar ba.
\”Wannan ba ya daga cikin batutuwan da za su tattauna,\” a cewarsa sabo da
A karshen watan jiya ne majalisar ta tafi dogon hutu bayan sauya shekar wasu \’yan majalisa fiye da 50 daga jam\’iyyar APC mai mulki zuwa PDP