An Samu Biliyoyi, Manyan Bindigu Da Dubban Katinan Zabe A Gidan Lawal Daura

0
651
Daga Usman Nasidi
RAHOTANNI na bayyana cewa an gano makudden kudade har N21 biliyan a gidan tsohon shugaban hukumar jami\’an tsaro na farin kaya (DSS), Mallam Lawal Musa Daura dake babban birnin tarayya, Abuja.
Wata majiya dake da masaniya kan lamarin tayi ikirarin cewa an gano bindigogi sama da 4000 tare da wasu kananan makamai da kuma katin zabe mallakar wasu bakin haure daga jamhuriyar Nijar duk a gidan nasa.
Ana tuhumar tsohon shugaban DSS din ta karkatar da wasu makuden kudade $21 miliyan da ya gada daga tsohon shugaban hukumar DSS, Mr Ita Ekpenyong.\’
A halin yanzu Daura na amsa tambayoyi game da kudin pansho N12.9 biliyan da aka fitar daga asusun ajiya ta hukumar na DSS. Ana kuma tuhumarsa da hannu cikin cire N1.6 biliyan daga asusun ajiyar inshora na ma\’aikatan hukumar, inji majiyar.
Sai dai babu wata kwakwarar majiya daga hukumar data tabbatar da afkuwar wannan lamarin saboda babu wanda yake son yin tsokaci kan babban batu irin wannan daya shafi tsohon shugaban hukumar ta DSS.
A ranar Alhamis data gabata, tsohon shugaban hukumar DSS, Ekpenyong ya bayyana a hedkwatan hukumar EFCC inda ya amsa tambayoyi kan yadda ya sarafa kudaden da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Kwanel Sambo Dasuki, ya bashi gabanin zaben shekarar 2015.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here