APC Ta Lashe Zaben Cike Gurbi A Katsina Da Kuri\’u 224, 607 Inda PDP tasami kuri\’u 59,724

    0
    643
    Rabo Haladu Daga Kaduna
    \’DAN takarar jam\’iyyar APC Ahmad Babba-Kaita ya doke dan uwansa Kabir Babba-Kaita na PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar dattawa da aka gudanar a Katsina ta arewa a ranar Asabar.
    Hukumar zabe ta ce Ahmad Babba-Kaita na APC ya samu kuri\’u 224,607, yayin da Kabir Babba Kaita na PDP ya samu kuri\’u 59,724.
    \’Yan uwan biyu sun fafata ne domin cike gurbin marigayi Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu a farkon watan Afrilun bana.
    An dai gudanar da zaben lafiya ba tare wani tashi hankali ba duk da zaben na \’yan gida daya ya ja hankali a Katsina da ma Najeriya baki daya.
    Hukumar zabe ta gudanar da zaben cike gurbi na \’yan majalisa a jihohi guda hudu da suka kunshi Katsina da Kogi da Bauchi ta kudu da jihar Kurus Ribas
    Sai dai kuma zaben jihar Kogi ya bar baya da kura inda rahotanni suka nuna cewar an samu matsalar satar akwatunan zabe da har ya janyo rasa rayuka.
    Rikici da Matsalar satar akwatunan zabe da sayen kuri\’u ne rahotanni suka ce suka mamaye zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya da aka gudanar a jihar Kogi.
    Rahotannin sun ce mutum biyu aka kashe a lokacin da ake zaben cike gurbin na dan majalisar tarayya da ke wakiltar Lokoja/Kogi da Koton Karfe.
    Rundunar \’yan sandan jihar ta tabbatar wa manema labarai ce an kashe mutanen biyu ne yayin da suka yi kokarin satar akwatunan zabe.
    Akwai runfunan zaben da kuma rahotanni suka ce \’yan bangar siyasa sun hana gudanar da Zabe.
    A jihar Bauchi kuwa, \’yan takara tara ne ke neman darewa kujerar sanatan gundumar kudancin jihar.
    \’Yan takarar sun hada da Lawal Yahaya Gumau (APC), sai Isah Yuguda (GPN), sai Haruna Ayuba (ADC), da Aminu Tukur (APP) da kuma Usman Hassan (Kowa Party).
    Sauran sun hada da Maryam Bargel (SDP) da Husseini Umar (NNPP) da Usman Chaledi (PDC) da kuma Ladan Salihu (PDP).
    A jihar Kurus Ribas da ke kudu maso gabashi  kuwa, an gudanar da zaben dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Obudu ne.
    Mazabar ba ta da wakili tun bayan mutuwar wakilinsu Mista Stephen Ukpukpen a karshen watan Mayun bana.
    Tuni dai aka gudanar da zabubbukan kuma a halin yanzu ana dakon sakamako ne a wadannan mazabu a sauran jihohin da aka gudanar da zaben cike gurbin.
    Hukumar zaben  ta bayyana cewa wadanda suka ka\’da kuri\’unsu sun zarce mutum miliyan biyu a cikin kanana hukumomi 22 na
    jihohi hudun.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here