Daga Usman Nasidi
A RANAR Litinin ne, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta rahotannin da kafafen yada labarai suka wallafa a kan cewar an samu makudan kudi da suka kai biliyoyi, daruruwan bindigu da dubban katinan zabe mallakin bakin haure daga jamhuriyar Nijar a gidan Lawal Daura, shugaban hukumar da aka kora daga aiki ba.
A cewar hukumar DSS, faifan bidiyon da aka samo labarin daga cikinsa na bogi ne, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito kakakin hukumar, Tony Opuiyo, na fada yau a Abuja.
“Babu gaskiya a cikin rahoton dake bayyana cewar an samu biliyoyi da bindigu da katinan zabe a gidan tsohon shugaban hukumar DSS, Lawal Daura. Hatta faifan bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna jami’an tsaro na bude wasu ma’adanai na kudi da nuna wasu manyan bindigu da sunan an same su ne a gidajen Lawal Daura dake Katsina da Abuja, ba gaskiya bane,” a cewar Opuiyo.
Sannan ya cigaba da cewa, “Muna sane da samun mabanbantan rahotanni da ake samu tun satin da ya gabata bayan hatsaniyar da ta faru a majalisa. Muna sanar da jama’a da su yi watsi da rahotanni da kuma faifan bidiyon dake nuna cewar an samu abubuwan da muka lissafa a gidan Lawal Daura.”
A yayin hutun karshen makon da muka yi bankwana da shi ne aka samu rahotanni dake yawo a garin kan cewar an samu makamai da makudan kudi da katunan zabe bayan birkice gidan Lawal Daura.