Cutar Kwalara Na Kara Kamari A Jihar Kano

0
796

 

Rabo Haladu Daga kaduna

 

MAHUKUNTA a jihar kano sun bayyana cewa akalla mutum dari uku ne suka harbu da cutar kwalara. Tun a farkon wannan shekarar ne cutar ta fara bulla, wadda da sannu ta shafi jihohi goma sha bakwai, ciki har daAbuja. Masana sun ce rashin tsabtar abinci da ruwan sha ne ke haddasa cutar ta kwalara.

A jihar Kano dubban mutane ne suka kamu da cuta mai alaka da amai da gudawa, amma kadan daga ciki ne aka tabbatar da cewa sun harbu da cutar kwalara, daga watan Janairun wannan shekarar zuwa watan Yulin da ya wuce.

Kwamishinan lafiyar jihar Kano, Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana haka, a wata ganawar da ya yi da manema labarai, inda wakilan kungiyoyin

gaji na kasa da kasa ciki har da wakilin Hukumar Lafiya ta duniya suka halarta. Yadda kwalara ke yaduwa a Najeriya Cutar Kwalara ta barke A Najeriyar dai kusan kowace shekara sai an samu bullar cutar kwalara, musamman ma a wannan lokaci na Damina.

Jihohin da cutar ta shafa a wannan shekarar sun hada da Adamawa da Anambara da Bauchi da Borno da Ebonyi da Gombe da Jigawa da Kaduna da Kano da Katsina da Kogi da Nasarawa da Neja da Filato da Yobe da Zamfara da kuma Abuja.

Bullar cutar kwalarar dai na kara fito da kalubalen da gwamnatoci ke fuskanta na samar da ingantaccen ruwan sha ga al`umma, da kuma bukatar ci gaba da wayar da kan jama`a a kan hanyoyin tsabtace kayan abinci.

Kodayake, jihar Kano a nata bangaren, tun bullar cutar, a farkon wannan shekarar ta fara gudanar da tarukan wayar da kan jama`a a kan cutar, da wasu sakonni ta kafafen yada labarai.

Sai dai alamu na nuna cewa akwai bukatar a matsa-kaimi, kasancewar a makon da ya wuce ma an samu mutum biyu da aka tabbatar da cewa sun harbu da cutar.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here