Daga Usman Nasidi
SHUGABAN majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Obasanjo inda suka shafe kusan sa’o’i biyu suna tattaunawa.
Saraki ya ziyarci Obasanjo ne a gidansa dake hade da dakin karatun da ya gina a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Saraki ya isa gidan na Obasanjo ne da misalign karfe 5:30 na yamma cikin bakar babbar mota kirar Toyota Land Cruiser tare da wasu jami’an tsaron sa kuma ya bar gidan da misalign karfe 7:12 na dare.
Tun da fari an shirya yin ganawar ne da misalign karfe 4:00 amma hakan bat a yiwu ba saboda Saraki bai samu isowa a kan lokaci ba.
Obasanjo da Saraki Bayan fitowar sa daga ganawar tasu ne, Saraki ya shaidawa manema labarai cewar ya ziyarci Obasanjo ne domin bai samu dammar halartar bikin bude dakin karatun da Obasanjo ya gina ba, wanda aka tun shekarar da ta gabata.
“Kun san ban samu dammar halartar bikib bude dakin karatun da Obasanjo ya gina ba, shi yasa yanzu na zo domin yi masa godiya bisa wannan aikin alheri sannan kuma nag a dakin karatun,” a cewar Saraki.
Da kamala fadin hakan ne kuma ya fada cikin motarsa tare da rufe kofa duk da manema labarai na yi masa ruwan tambayoyi, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Wata majiya ta bayyana cewar ganawar ta Saraki da Obasanjo na da nasaba da rigingimun dake tsakanin bangaren ‘yan majalisa da na zartarwa, musamman yunkurin tsige Saraki da sanatocin APC karkashin jagorancin Oshiomhole ke shirin yi.