Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kaduna Ya AJIYE Aikinsa

0
546

 

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

MATAIMAKIN shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna Mista John Audu Kwaturu ya sauka daga mukamin mataimakin shugaban majalisar.

Faruwar hakan dai baya rasa nasaba da barin Jam\’iyyar APC da mataimakin shugaban majalisar ya yi a ranar Jama\’a.

Ya dai bayyana dalilin barin ajiye matsayin nasa ne da cewa ya yi ne saboda irin gazawar da jam\’iyyar ta yi na rungumar mutanensa da suka fito daga kudancin Jihar.

Ya dai Mika takardar ajiye aikin ne a yau 14/08/2018 inda ya mikawa ofishin shugaban majalisar. Nan gaba kadan zamu kawo maku Karin bayani idan akwai.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here