Rabo Haladu Daga Kaduna
A CEWAR Hariya wannan Baban takaicine a tsarin rayuwar Bahaushe, kuma abin kunya ne a ce mace ta yi ciki ba tare da aure ba.
Hakan ce ta sa idan har irin wannan kaddara ta fada wa wasu, sai su yi duk kokarin da za su yi don gujewa haifar cikin. Haka wata baiwar Allah a birnin Kano, wacce ta fayyacewa manema labarai wani al\’amari da ya faru da ita shekara 12 da suka gabata, na yadda ta yi ciki ba aure ta kuma haifi dan, amma saboda gudun abin kunya
sai ta dauki wani mataki da ya sa ta da-na-sani tun ba a je ko ina ba.
Wannan baiwar Allah da muka boye sunanta na gaskiya muka sa mata suna Hariya, ta ce ta tsinci kanta a wani mummunan yanayi yayin da aka wayi gari ta ganta dauke da ciki ba tare da ta yi aure ba.
Hariya mai shekara 35 ta ce tana da shekara 23 ne wani mutum ya yaudare ta ya yi mata ciki, kuma daga baya ya kekasa kasa ya ce cikin ba nasa ba ne.
\”Lokacin da na samu cikin na sha wahalar da ban taba tsammanba zan rayu ba, iyayena suka kore ni, sai na koma gidan yayar mahaifina na zauna a can har na haihu.
\”Manyana sun so a zubar da cikin don har mun je asibiti, amma sai aka ce ina iya rasa raina sakamakon haka. Wannan tsoron ne ya sa na ce gaskiya abar min cikin kawai.\” Yaya aka yi da dan?
Hariya ta ce bayan kwanaki kadan da haihuwarsa sai ta faki idon mutane ta kai shi kofar wani gida ta ajiye shi, ta juya ta tafi.
\”Amma da na koma gida sai tunani da damuwa suka shige ni, sai na shaida wa yayar mahaifina cewa na kai yaron nan wani gida amma kuma yanzu na kasa samun nutsuwa.
\”Sai muka je don dauko yaron, sai muka samu har an yi cincirindo ana ta ganin dan da kuma jimamin yadda aka jefar da shi,\” in ji Hariya.
Ta ci gaba da cewa: \”Da kyar suka yarda suka ba mu dan bayan sun ja min kunne kan rashin kamatar abun da na yi.\”
Rashin aure duk da cewa Hariya ta yi da-na sanin abun da ta yi, amma har yanzu shekara 12 bayan hakan ba ta yi aure ba.
Ta alakanta hakan da yadda ake kyamar auren duk wacce ta taba haifar dan da ba na sunna ba a kasar Hausa, duk kuwa da tarin nadamarta.
Sai dai ta ce ita wannan ba ya damunta, a yanzu burinta shi ne ta yi wa danta kyakkyawar tarbiyya ta kuma taimaka wajen ba shi ilimi ta yadda rayuwarsa ba za ta tagayyara ba.