GWAMNATI TA SAKE FARFADO DA MAKARANTUN ALLO DA AKA BUBBUDE A NIJERIYA-YUSUF YAHAYA  

0
182

 

Isah Ahmed, Jos

 

SHUGABAN kungiyar malaman makarantun Islamiyya ta jihar Filato [Ittihadu Anwaril Hidayat] Alhaji Yusuf Yahaya ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake farfado da makarantun Allo da aka giggina a wasu jihohin arewacin kasar nan, a zamanin gwamnatin da ta gabata.

Alhaji Yusuf Yahaya ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron karawara juna sani da kungiyar ta shiryawa malamai da iyayen yara da dalibai a garin Jos.

Ya ce ‘babu shakka wadannan makarantu suna da matukar mahimmanci, domin ana killace almajirai ana basu abinci maimakon yawon barace baracen da suke yi.

Ya kara da cewa idan wannan gwamnati ta rungumi wadannan makarantu ta kara gina wasu a kasar nan za a magance matsalar almajiranci a kasar nan.

Yahaya ya yi bayanin cewa sun shirya wannan taron karawa juna sani ne don gano dalilan da suka sanya makarantunsu suka tabarbare tare da gano hanyoyin magance matsalolin da suke damun makarantun.

Ya ce “a wannan taro sun gano cewa malamai suna kin zuwa makarantu ne saboda iyaye basa biyan kudaden makaranta kuma basa karfafawa yaran gwiwar zuwa makarantun ta hanyar biyan masu kudaden makaranta da saya masu litattafai.

Don haka sun jawo hankalin iyaye kan hakkokin dake kansu na karfafawa yaransu gwiwa kan neman ilmi ta hanyar biyawa yaran kudaden makaranta tare da saya masu kayayyakin karatu.

A nasa jawabin Na’ibin babban Limamin Jos Sheikh Gazali Isma’ila Adam  ya yi kira ga dalibai su zamanto  masu hakuri da juriya da biyayya  a kowanne lokaci.

Har’ila yau ya yi kira ga iyaye su rika karfafawa yaransu gwiwa wajen biyan kudaden makaranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here